
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta yi rashin mai magana da yawunta, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya rasu a safiyar yau Laraba bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.
An tabbatar da mutuwarsa ne a wata takarda da aka aike wa manema labarai a Kano daga Shugaban ofishin hukumar na Ƙaramar Hukumar Ɗambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru. A cewar sanarwar, an gudanar da jana’izar marigayin ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Laraba.
Marigayin ya kasance kakakin hukumar a jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen harkokin sadarwa da ayyukan bayar da agajin gaggawa na hukumar ga al’umma. Abdullahi ya shahara da yaɗa labarai akan kari waɗanda suka shafi lamuran gobara, matakan kariya, ayyukan bada agajin gaggawa da wasu harkoki da nufin bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
An bayyana wannan al’amari a matsayin babban rashi ga hukumar da kuma ɗaukacin mazauna Kano musamman bisa la’akari da yadda yake ƙoƙarin sanar da mutane halin da ake ciki akan lokaci yayin lamuran gaggawa.
Tuni dai abokan aiki da sauran masu ruwa da tsaki suka shiga jimamin rashin marigayin, da kuma tunatar da gudummawar da ya bayar wajen amincin al’umma da sanarwar gaggawa. Mutuwar jami’in ta zo ne a matsayin rashi ga ƙoƙarin hulɗa da jama’ar hukumar, wanda ya kasance mai aiki a matsayin ɗan tsakiya tsakanin hukumar da al’umma yayin iftila’in gobara da wasu lamuran gaggawa.
