Kwamishinan lafiya na Nasarawa yabawa sabuwar sakatariyar NASPHFIRA kan Inganta kiwon lafiya

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Kwamishinan Lafiya na Jihar Nasarawa Dakta Gaza Gwamna, ya bayyana hukumar kula da asibitocin masu zaman kansu da cibiyoyin lafiya ta Jihar Nasarawa wato NASPHFIRA a matsayin hukuma mai matuƙar muhimmanci ga ma’aikatar lafiya baki ɗaya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da babbar sakatariyar zartarwa ta hukumar Dakta Nana Awaya Emeribe ta jagoranci tawagarta domin kai masa ziyarar sada zumunta.

A ƙoƙarin samar da haɗin gwiwa a tsakanin ma’aikatu da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki Dakta Emeribe ta gabatar da tsarin aikin hukumar ga kwamishinan tare da tattauna dabaru don tabbatar da gudanar da aiki cikin sauki.

Da yake taya Dakta Emeribe murna kan naɗin ta a matsayin babbar sakatariyar zartarwar ta farko ta hukumar, kwamishina Gwamna ya ce babban nauyi ya rataya a kanta.

“Ina taya ku duka murna, wannan sabuwar hukuma ce, kuma a matsayinku na waɗanda suka fara aikin, babban nauyi ya rataya a kanku. Hukumar za ta nuna irin mutanen da kuke,” in ji shi.

Dakta Gwamna ya jaddada muhimmancin haɗin kai, aiki tare da fahimtar juna wajen cimma muradun hukumar, inda ya ce nasara ba za ta samu ba sai idan shugabanci ya ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin mambobi.

Ya yi gargadi cewa, “Idan manufar neman biyan buƙatar kai ce kawai, hakan zai haifar da jinkiri. Haka kuma duk wani alamar son kai zai ja mu da baya, kuma kafin ku ankara, wa’adinku na shekaru huɗu zai ƙare.”

Da yake magana kan ƙalubalen da hukumar za ta fuskanta, Dakta Gwamna ya amince da muhimmiyar rawar da NASPHFIRA ke takawa wajen yaƙi da masu yin angulu da kan zabo da kuma ayyukan bogi a asibitocin masu zaman kansu, inda ya buƙaci tawagar da ta jajirce wajen tsaftace harkar lafiya mai zaman kanta a jihar.

“Wannan hukumar tana da matukar muhimmanci a gare ni. Da ace ina da iko, da na kori duk wanda ya yi ba daidai ba nan take, domin muna da burin cimma abubuwa da yawa a cikin kankanin lokaci,” ya jaddada.

Bugu da ƙari, Dakta Gwamna ya ƙarfafa tawagar NASPHFIRA da ta mayar da hankali kan ayyukan da za su ba ta suna mai kyau saboda sauye-sauye masu kyau da ta kawo a fannin lafiya kafin ya sauka daga muƙaminsa na kwamishinan lafiya.

A nata jawabin, Dakta Nana Awaya Emeribe ta bayyana cewa ma’aikatar lafiya ita ce ma’aikatar da ke kula da NASPHFIRA, inda ta ce ziyarar tasu kamar komawa gida ce domin neman shiriya da shawarwarin kwamishinan kan ayyukansu.

By ukarofi

Leave a Reply