Sin ta buƙaci haɗin gwiwar ɓangarori daban-daban don hana yaduwar makaman nukiliya

Daga CMG HAUSA

Zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Zhang Jun ya ce, hana yaduwar makaman nukiliya wani babban ƙalubale ne na kasa da ƙasa. Domin daidaita wannan batu, akwai buƙatar a tabbatar da haƙiƙanin haɗin gwiwar ɓangarori daban-daban, kuma jagorancin MƊD na da matuƙar muhimmanci game da wannan batu.

Zhang Jun ya bayyana hakan ne a yayin buɗe taron tuntubar juna game da yin cikakken nazari domin aiwatar da ƙudurin kwamitin sulhun MƊD mai lamba 1540, da farko wannan ƙuduri ya dora alhakin wajabtawa dukkan ƙasashe mambobin kwamitin sulhun MƊD, da su yi kokarin dauka tare kuma da aiwatar da kwararan matakan yaƙi da bazuwar makamai a tsakanin al’umma waɗanda ake amfani da su wajen tafka mummunar ɓarna wato (WMDs), sannan a yi ƙoƙarin daƙile hanyoyin da ake jigilarsu, da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen ta da rikici.

Game da wannan batu, ya buƙaci a tabbatar da hadin gwiwar ɓangarori daban-daban a bisa gaskiya.

Da yake bayani game da yadda za a tabbatar da hadin gwiwar ƙasa da ƙasa don tinkarar batun hana bazuwar makamai a duniya, Zhang Jun ya bayyana cewa, hana yaɗuwar makaman nukiliya NPT shi ne ƙashin bayan shirin hana yaɗuwar makamai na ƙasa da ƙasa, kuma hakan wani muhimmin jigo ne wajen daidaita matsalar tsaron ƙasa da ƙasa daga barazanar ɓarkewar yaƙi.

Jakadan ya kuma buƙaci yin amfani da kimiyya da fasaha don tabbatar da zaman lafiya da kuma gudanar da hadin gwiwar ƙasa da ƙasa kan wannan batu, wanda ya kasance haƙƙi ne na wajibi da ya rataya a wuyan kowace ƙasa bisa tsarin dokokin ƙasa da ƙasa.

Mai fassara: Ahmad Fagam