Yadda haɗin gwiwar Sin da Afirka ke ƙara cigaban ƙasashen Afirka

Daga IBRAHIM YAYA

Layin dogo yana daya daga cikin muhimman ababen more rayuwa da ƙasashen nahiyar Afirka suka amfana da shi, ƙarƙashin haɗin gwiwar Sin da ƙasashen na Afirka, baya ga hanyoyin mota, da gadoji na zamani, da makarantu da cibiyoyin lafiya da makamantansu.

Tun bayan ƙaddamar da layin dogo na zamani na SDR a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2017 tsakanin Mombasa zuwa Nairobo, da ƙasar Sin ta gina, shekaru biyar da suka gabata, yanzu haka ƙasar Kenya ta shiga wani sabon tsari na rayuwa, inda ya sauya harkokin sufuri, da kasuwanci da nishaɗi a ƙasar Kenya.

Bayanai na nuna cewa, layin dake tafiyar da jiragen ƙasa na fasinja guda shida a kullum, ya yi nasarar jigilar fasinjoji sama da miliyan 7.7 a cikin shekaru biyar din da suka gabata. Kana a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2022, adadin fasinjojin da aka yi jigilar su ta hanyar layin dogon na zamani, ya kai 962,000, wanda ya kai kashi 63 cikin dari a duk shekara.

Haka kuma, a cikin shekaru biyar da suka gabata, layin dogon ya yi jigilar sama da Tan miliyan 1.7 na kwantenoni. Kana yawan kayayyakin da jirgin ƙasan dakon kaya ya yi jigilarsu a cikin watanni biyar da suka wuce, ya kai tan miliyan 2.54, ƙaruwar kashi 8.3 bisa dari a shekara.

Layin dogon ya kuma samar da wata kafa ga matasan Kenya, wajen bunkasa fasaha da sana’o’insu da samun kuɗin shiga, da inganta fasaha da samar da aikin yi da raya manyan sassan tattalin arzikin ƙasar kamar aikin gona, da masana’antu da yawon shakatawa.

Baya ga layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, akwai na Tanzaniya zuwa Zambia (Tazara) da wadanda Sin ta gina a sassan daban-daban na Najeriya da sauran ƙasashen Afirka, kuma duk sun taimaka wajen sauƙaƙa jigilar jama’a da hajoji tsakanin ƙasashen nahiyar, baya da samar da guraben ayyukan yi da karin kuɗaɗen shiga ga mazauna waɗannan yankuna, galibi matasa.

Sabon ɗakin taro na zamani da ƙasar Sin ta samar da kuɗin ginawa da aka ƙaddamar a Zambia a baya-bayan nan, ya ƙara nuna cewa, alaƙar Sin da Afirka, alaka ce ta amintakar ƙut-da-ƙut kut da mutunta juna da samun nasara tare. Kuma duk ƙoƙarin da wasu ƙasashen yamma ke yi na neman illata wannan dangantaka, ba zai taba yin nasara ba.