Kotun Maiduguri ta bada belin mutum biyar da aka tsare kan rigar TMG

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Kotun Shari’a a Maidugurin Jihar Borno ta bayar da belin wasu mutane biyar da aka kama su bisa sanya riguna masu ɗauke da rubutun #TinubuMustGo (TMG).

An kama mutanen ne a ranar 25 ga Satumba, 2026 a cikin garin Maiduguri, lamarin da ya tayar da ƙura musamman a kafafen sada zumunta kan ‘yancin bayyana ra’ayi da mutunta tafiyar siyasa a jihar.

Saidai rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ta yi iƙirarin cewa ta kama waɗanda ake zargin ne da wasu laifuka akan ra’ayin siyasa ds wasu ke zargi, wannan ci-gaba ya haifar da cece-kuce acikin al’umma. A cewar ‘yan sandan, jami’ai sun ƙwato ƙulli 15 na tabar wiwi, ƙwayar D5 guda 100, tukunyar busa hayaƙin shisha, almakasai da wasu rigunan TMG biyu.

Yayin da mutane da dama suke sukar mahukunta da yunƙurin tauye ‘yancin masu zanga-zangar lumana saboda bambance-bambancen siyasa, rundunar ‘yan sandan ta musanta waɗannan zarge-zarge. Ta bayyana cewa, har yanzu tana nan akan biyayya ga hukuncin doka da ya haramta mata da jami’anta ɗaukar ɓangare a lamuran siyasa kuma ta damƙa al’amarin ga fannin shari’a domin tabbatar da cewa an bi hanyoyin da doka ta tsara wajen hukunci kan al’amarin.

An kuma alaƙanta wannan batu da Gwamna Umara Babagana Zulum bisa zargin cewa yana da hannu a kama mutanen. Saidai, a wata takarda da gwamnatin jihar ta fitar ta ofishin mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, gwamnatin ta musanta tare da yin watsi da iƙirarin, inda ta ce ba gaskiya ba ne. Gwamnatin ta bayyana cewa Gwamna Zulum bai taɓa ambaton ƙungiyar TMG ba, ADC ko wani ɓangaren siyasa a hirarraki da ake yi da shi, saidai ya fi mayar da hankali akan tsaro, zaman lafiya da kiyaye doka da oda.

Barista Alƙali Askira, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) reshen Garki, ya tabbatar da sako mutanen. Sannan ya gargaɗi matasan da su cigaba da kasancewa masu biyayya ga doka da oda yayin da iyalansu a gefe guda suka miƙa saƙon godiyarsu ga tawagar lauyoyin da suka tsaya wa ‘ya’yan nasu da kuma kira ga matasa a jihar da su kasance masu biyayya ga doka da oda.

By Babaji

Leave a Reply