Daga BASHIR ISAH
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa yanzu ba su da wani aiki a gabansu da ya wuce na tabbatar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a APC, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai bantensa a zaɓen 2023.
Adamu ya ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin ziyarar da shi da tawagarsa suka kai wa Tinubu a gidansa da ke Abuja ranar Alhamis don taya shi murnar lashe zaɓen fid-da gwani na APC da ya yi a Larabar da ta gabata.
Da yake yi wa manema labarai jawabi yayin ziyarar, Adamu ya ce, “Mu dai mun yi an kuma gani a ƙasa, mun zo nan ne don taya ɗan uwanmu murna, sannan mu tabbatar masa cewar muna tare.
“Wannan aikinmu ne, kuma da yardar Allah za mu yi nasara,” inji shi.
Bayanai sun nuna cewa tun bayan da Tinubun ya yi nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC, yake fama da karɓar baƙi a gidansa, kama daga jam’ian jam’iyyarsu ta APC zuwa sauran mambobin jam’iyyar da masoya da magoya baya da sauransu, don taya shi murna.
A nasa ɓangaren, Tinubu ya yi godiya da ziyarar, tare da yaba wa kwamitin kan nasarar da ta samu wajen shirya zaɓen cikin nasara.
Daga nan, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su haɗa kai su yi aiki tare domin samun zarafin yin galaba a kan abokan hamayyarsu yayin zaɓen 2023.
