Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron shugabannin BRICS karo na 14 da ya gudana a daren jiya, ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, faɗar mulkin ƙasar. Yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Xu, ya ce taron ya gudanar cikin nasara, wanda ke da muhimmiyar ma’ana ga makomar ƙungiyar.
Ma ya furta cewa, a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Xi, shugabannin ƙasashen BRICS sun tattauna sosai kan yadda za a raya kyakkyawar hulɗar abota, a kokarin sa kaimi ga ci gaban duniya. Haka kuma Shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan haɗin gwiwar ƙasashen BRICS, waɗanda suka ɓullo da dabarun raya kyakkyawar hulɗar abota a tsakaninsu, lamarin da ya samu karɓuwa daga ɓangarori daban daban.
Bugu da ƙari, Ma ya bayyana cewa, an zartas da Sanarwar Beijing ta taron, inda aka bayyana matsayin ƙasashen BRICS na bai ɗaya kan wasu muhimman batutuwan shiyya-shiyya da na duniya, da nuna sakamakon haɗin kansu, kana da tsara shirye-shiryen hadin gwiwarsu a nan gaba.
Ma ya ƙara da cewa, ƙungiyar ƙasashen BRICS wata muhimmiyar alama ce ta ci gaban ƙasashe masu tasowa. Ya zuwa yanzu dai, ƙasashen BRICS sun riga sun hada kansu har na tsawon shekaru 16, lamarin da ya zama abin koyi ta fuskar haɗin kan ƙasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa.
Bana ita ce karo na uku da ƙasar Sin ta karbi baƙuncin taron shugabannin BRICS, inda aka samu dimbin sakamakon haɗin gwiwa na a zo a gani a fannonin farfaɗowar tattalin arzikin duniya, daƙilewa da rigakafin yaɗuwar cutar COVID-19, da raya tattalin arziki bisa fasahar zamani, da neman samun ci gaba mai ɗorewa, da mu’amalar al’adu. Don haka ƙasar Sin ta bayar da gudummawarta ga ci gaban haɗin kan BRICS. Taron dai ya buɗe wani sabon babi ga haɗin kan ƙungiyar, wanda ya nuna kyakkyawar makomar tsarin haɗin kansu.
Mai fassara: Kande Gao
