Masari ya ɗauki nauyin Kiristoci 28 zuwa aikin ibada ƙasar Isra’ila

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta ɗauki nauyin mabiya addinin Kirista ‘yan asalin jihar zuwa ƙasar Isra’ila da kuma Jordan don gudunar da aikin ibadarsu.

Kamar yadda Manhaja ta samu, Kiristocin waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na jihar za su je ƙasar Isra’ila ne da ƙasar Jordan domin ziyarar wuraren ibadarsu da kuma wuraren tarihi masu muhimmanci a addinin na su.

Da yake ƙarin haske a kan batun ga majiyar Manhaja ta Katsina Post mai bai wa gwamnan jihar shawara akan addinin Kiristocin, Rabaran Ishaya Jimrau, ya bayyana cewa mutanen da gwamnatin ta ɗauki nauyi sun haɗa da jami’an gwamnati, malaman addinin Kiristocin da kuma shugabanninsu na majami’u daban-daban.

Rabaran Ishaya ya kuma ƙara da cewa wasu Kiristocin su 28 daga jihar sun biya ma kansu kuɗin zuwan kuma da su za a tafi.

Daga ƙarshe sai ya gode wa gwamnan tare da shan alwashin za su cigaba da bayar da cikakken goyon bayansu ga cigaban gwamnatin a dukkan matakai.