Bauchi ta zaƙulo ma’aikatan bogi 8,211 da samun rarar kuɗi Naira biliyan ɗaya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta zaƙulo ma’aikatan bogi 8,211 tare da kuma samun rarar kuɗi har sama da Naira biliyan ɗaya.

Wani mai shekaru 71 da haihuwa yana ɗaya daga cikin ma’aikatan bogi 8, 211 da gwamnatin Jihar Bauchi ta zaƙulo a cikin jerin sunayen ma’aikatanta, kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Mohammed Kassim ya zayyana.

Kassim ya kuma bayyana bambancin alƙaluman kuɗaɗen albashin ma’aikatan gwamnatin jihar ta yadda aka samu wannan rarar ta maƙudan kuɗaɗe, inda yake cewa lokacin da suka hau karagar mulki, kuɗaɗen albashin ma’aikata yana laƙume zunzurutun kuɗaɗe Naira biliyan shida da ɗigo bakwai, amma yanzu da gwamnatinsu ta sanya rariya ta tace kimanin yawan ma’aikatanta, kuɗaɗen albashin ya faɗi ƙasa zuwa Naira biliyan biyar da ɗigo bakwai.

Wannan kamar yadda ƙididdigar ta nuna, lokacin da gwamnati mai ci ta hau mulki, albashin ma’aikata yana laƙume Naira biliyan uku da rabi, amma yanzu bayan bin ƙwaƙƙwafin yawansu, kuɗaɗen biyan albashi ya faɗi ƙasa zuwa Naira biliyan biyu da ɗigo takwas, yayin da albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi guda 20 kuwa ya faɗi daga Naira biliyan uku da ɗigo biyu zuwa Naira biliyan biyu da ɗigo tara.

Barista Ibrahim Kassim ya shaida wa taron manema labarai a garin Bauchi a ranar Litinin da ta gabata cewar, adadin yawan ma’aikatan gwamnatin jiha ya faɗi daga mutum 32,000 zuwa 28,789, yayin da na ƙananan hukumomi kuwa ya faɗi daga 53,000 zuwa mutum 48,000, lamarin da ya nuna ma’aikatan bogi guda 8,211 kenan.

Kassim wanda yake jawabi kan sakamakon rahoton kwamitin tantance yawan ma’aikatan jiha na mataimakin gwamnan jiha, Sanata Baba Salihu Tela, ya bayyana damuwarsa bisa tsinkayar wani ma’aikaci mai shekarun haihuwa 71 yana maƙale a cikin aikin gwamnati yana karɓar albashi na wata-wata, wanda kamata ya yi a ce ya yi ritaya yayin cika shekaru 60 da haihuwa, ko shekaru 35 na wa’adin aikin gwamnati.

Kassim sai ya bayar da tabbacin cewar, duk wasu matsaloli ko batutuwa da suka yi tarnaƙi wa biyan albashin ma’aikatan jiha za a samu warwarar su dagan nan zuwa watan Yuli mai gabatowa, lokacin da ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati za su karɓi alhakin biyan albashin ma’aikatansu, ba baitulmali ba.

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma nuna takaicinsa bisa yadda gwamnatinsu ta gaji wani tsarin biyan albashi mai cike da almundahana da aka shafe shekaru kusan arba’in ana wakaci-katashi da kuɗaɗen jama’a, haɗe da hauhawar kuɗaɗen biyan albashi, tamkar babu ma’aikata masu yin ritaya, mutuwa ko canjin aiki, ana nan a sojan badakkare.

Kassim ya ce: “Daga yanzu ofishin Shugaban Ma’aikata na jiha shi ke da alhakin adana jerin ma’aikatan jiha, wanda yake da nufin cewar, lokacin da ma’aikatu, hukumomi ko sassan gwamnati za su ɗauki mutum ko mutane yin aikin gwamnati ba tare da tuntuɓar ofishin shugaban ma’aikata ba, ya shuɗe, ko ya zama tarihi.

“Kuma halayya, yanayi ko zamani na samun ma’aikacin bogi a ƙananan hukumomi, na idan ma’aikaci ya mutu ko ya yi ritaya a cusa sunan wani a gurbinsa shi ma ya zama tarihi. An horas da jami’an ƙananan hukumomi ta yadda za su riƙa biyan albashin ma’aikatansu. Maganar da nake yi a halin yanzu, babu wani ma’aikaci a cikin dukkan ƙananan hukumomi guda ashirin na jiha dake ƙorafin baya samun albashi,” inji Kassim.

Ya ce, Bauchi tana tutiyar cewa, wannan jiha a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, tana ɗaya daga cikin ‘yan ƙalilun jihohi a cikin tarayyar ƙasar nan da suke biyan albashin wata-wata, babu kace-nace, ya qara da cewar, “a ƙaramar sallah da ta gabata, Bauchi ita ce jiha ɗaya ƙwal da ta biyan albashin ma’aikata gabanin Sallar Eid-el fitr,” inji Kassim.

Kassim ya kuma yi tir da waɗanda suke neman shafa wa gwamnati kashin kaji domin neman yin bajintar siyasa, su kwana da sanin cewar, wannan cakwara da ta dabaibaye biyan albashin ma’aikata shekaru aru-aru, da ta zame wa gwamnatocin baya gagara-gasa, gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ta kawar da shi, kuma hanya ta miƙe sarmadan, “don haka, gwamnatinmu ta taka rawar gani,” inji shi.