Wani matashin baƙar fata kuma Ba-Amurke da aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 1931 saboda kisan wata farar fata, wata kotu a Pennsylvania ta wanke shi a wannan makon, bayan shafe shekaru da dama ‘yar uwarsa ɗaya tilo tana bibiya.
Wani alƙali farar fata ne ya yanke wa Alexander McClay Williams mai shekaru 16 a lokacin hukunci cikin sa’o’i huɗu kacal, kuma ya kasance mafi ƙarancin shekaru da tava yankewa hukuncin kisa a jihar ta gabashin Amurka.
Amma bayan shekaru 91, wani alƙali ya yi watsi da ƙarar kuma ya bayyana Williams ba shi da wani laifi.
’Yar uwar Williams ɗaya tilo da ta rage masa, Susie Williams-Carter, ta mai da martani ga ci gaban a ranar Alhamis, 16 ga Yuni, 2022, ta ce, “na yi farin cikin cewa a ƙarshe an wanke shi kamar yadda ya kamata ya kasance a farkon.
“Muna son a wanke shi ne kawai saboda mun san ba shi da laifi, kuma yanzu muna son kowa ya san hakan,” inji ’yar shekaru 92.
Lauyan gundumar Delaware Jack Stollsteimer ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an yi watsi da qarar a ranar Litinin, bayan shafe shekaru ana shari’a.
Sanarwar ta ce, “shari’ar gaba ɗaya bai kamata ba, bai kamata a taɓa gabatar da tuhumar da ake yi masa ba in a farko.”
Shari’ar ta nuna rashin adalci na wariyar launin fata na tarihi a tsarin dokokin Amurka, wanda aka yanke masa hukunci kuma a lokuta da dama an kashe Amurkawa marasa laifi, da yawa daga cikinsu baƙar fata ne, a ƙarnin da ya biyo bayan yaƙin basasa na 1861-1865.
