Kashi na farko na kayayyakin agajin girgizar ƙasa da gwamnatin ƙasar Sin ta taimaka sun isa birnin Kabul

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, kashi na farko na kayayyakin agajin girgizar ƙasa da gwamnatin ƙasar Sin ta taimakawa Afganistan suka isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, babban birnin ƙasar Afganistan. Jakadan ƙasar Sin dake Afghanistan Wang Yu, da Gholam Gaus, muƙaddashin ministan kula da bala’o’i da ayyukan jin kai na gwamnatin wucin gadin ƙasar Afghanistan, sun halarci bikin miƙa kayayyakin.

A jawabinsa jakada Wang Yu ya bayyana a yayin bikin mika kayayyakin cewa, girgizar ƙasar da ta afkawa ƙasar Afganistan, ta taba zukatan jama’ar ƙasar Sin, kuma nan take gwamnatin ƙasar Sin ta yanke shawarar ba da taimakon jin kai na gaggawa da darajarsa ta kai Yuan miliyan 50 ga yankin da bala’in ya shafa.

A cikin kwanaki uku masu zuwa, jiragen sama na ƙasar Sin guda 6, za su ci gaba da kai kayayyakin agaji. Haka kuma, dukkanin kayayyakin abinci da kasar Sin ta yi alƙawarin taimakawa Afghanistan, sun riga sun isa tun ‘yan kwanakin da suka gabata, kuma yanzu haka, an ƙara saurin rarraba kayayyakin abinci.

A nasa ɓangaren Gholam Gaus ya bayyana cewa, abubuwa da ƙasar Sin ta yi, yana nuna irin kyakkyawan zumuncin dake tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu na tsawon dubban shekaru.

Fassarawar Ibrahim