Kotu ta yi watsi da sabon belin da Nnamdi Kanu ya nema

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya da Ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Alƙali Binta Nyako, ta yi watsi da batun belin da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya kuma nema.

A zaman shari’ar da kotun ta yi ranara Talata, Mai Shari’a Nyako ta ce sake neman belin da Kanu ya yi tamkar cin mutunci ne ga kotu.

Ta ce, buƙatar da Kanu ɗin ya gabatar wa kotun wani yunƙuri ne na maida wa kotu hannu agogo baya kan batutuwan da an rigaya an yanke hukunci a kansu.

Ta kuma tsaya kai da fata kan lallai sai Kanu ya ba da dalilin da suka sanya shi saɓa ƙa’idojin belin da aka ba shi a baya kafin ya sake samun wata damar.

Sai dai Nyako ta shawarci Kanu a kan ya ɗaukaka ƙara idan har yana ganin bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Ta ce tun bayan da aka ba da belin Kanu a Yulin 2017, an ɗage shari’arsa har sau 15 kuma har yanzu ƙarar ba ta samu muhimmin sauraro ba.

Ta ƙara da cewa, sam ba ta gamsu da dalilan da Kanu ya gabatar na rashin halartar kotun ba.

Daga nan, Aƙalin ta ɗage shari’ar zuwa ranar 14 ga Nuwamba don ci gaba da shari’ar da kuma dakon sakamakon ɗaukaka ƙararsa.