Gwamnatin Tarayya za ta amshe ragamar tafiyar da filayen jiragen sama daga jihohi

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ƙudurinta na amshe ragamar tafiyar da harkar sufurin wasu filayen jiragen sama daga hannun gwamnatocin jihohi.

Hadi Sirika, Ministan harkar sufurin jiragen sama, shi ya bayyana haka a yayin taron ƙara wa juna sani na hukumar sufuri a sararin samaniya (FAAN) wanda aka gudanar a Abuja.

A cewar Sirika, filayen jiragen saman da gwamnatin Tarayyar za ta ƙwace su ne, na jihohin; Kebbi, Jigawa (Dutse), Bauchi da kuma Gombe.

Sannan ya ƙara da cewa, da yawa ma daga filayen jiragen saman da suke mallakin jihohi a Nijeriya za a amshe su daga hannun jihohi a miƙa wa ‘yan kasuwa ragamar cigaba da tafiyar da su yadda ya kamata.

“Ƙasar Nijeriya tana da jimillar filayen jiragen sama guda 43. Daga cikin waɗannan filayen jiragen saman guda 43, wasu mallakin gwamnatin Tarayya ne, wasu mallakin jihohi ne, yayin da wasu kuma mallakin ‘yan kasuwa ne”.

A dai cikin jawabin nasa, Sirika ya ƙara da cewa, Gwamnatin tarayya ta ɗaura ɗamarar kawo sauyin da cigaba a ɓangaren harkar sufurin jirgin sama a Nijeriya. Kuma akwai wasu sabbin tsare-tsare da hukumar ke son gudanarwa kafin nan kafin ƙarshen wa’adin mulkin Buhari.

Da wannan ya ce yana ƙalubalantar ‘yan kasuwa da su zuba jari a harkar sufurin jirgin saman. Domin a cewar sa harka ce mai matuƙar albarka da samun mafita. Don haka a cewar sa, dama ce ta zo musu har gida wacce ya kamata su dama ta.