Buhari ya karrama tsohon Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko da lambar yabo

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya karrama tsohon Alƙalin Alƙalan Nijeriya wanda ya yi murabus kwanan nan, Ibrahim Tanko da lambar yabo ta ƙasa, wato GCON.

Wannan ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata a wajen taron rantsar da Jastis Olukayode Ariwoola a matsayin Muƙaddashin Alƙalin Alƙalai na Nijeriya da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Da yake jawabi a wajen taron, Buhari ya ce ya karrama Jastis Ibrahim Tanko da lambar yabon ne bisa la’akari da aiki tuƙuru da ya yi wa ƙasa a lokacin da yake riƙe da muƙamin Alƙalin Alƙalai.

Buhari ya ƙara da cewa, fannin shari’a ya yi aikinsa daidai da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 a ƙarƙashin jagorancin Tanko.

Lambar yabo ta ‘GCON’, ita ce lamaba mafi girma ta biyu wadda akan bai wa duk wani ɗan ƙasa da ya cancanta.

A kwanan nan ne Ibrahim Tanko ya yi murabus daga muƙamin Alƙalin Alƙalai saboda dalili na rashin lafiya, inda Buhari ya maye gurbinsa da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mai riƙon ƙwarya.