Rayuwar Ahmadu Bello Sardauna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamar dai yadda muka fara, jaridar Blueprint Manhaja za ta ci gaba da kawo wa mai karatu tarihin wasu fitattun mutane, domin kuwa tarihi wata babbar makaranta ce da ke cike da ɗimbin darrusa da mai karatu zai iya koya musamman idan aka ce ya shafi rayuwar wani mutum.

Tabbas, Sir Ahmadu Bello wanda shahararren mawaƙi shata ya siffanta da Gamji Uban ’yan Boko, mai tawakkali gun Allah… ya cancanci wannan yabo. Wannan mutum haziƙi ne kuma jarumi wanda rayuwarsa ke cike da darrusan da suka kamata a koya.

Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato basarake ne, malamin makaranta, kuma ɗan siyasa, mai kishin ƙasa da jama’arsa. Ya rayu a ƙarƙashin mulkin mallakar Turawa har zuwa farkon samun mulkin kai. A saboda haka akwai ɗimbin darrusa da za a iya koya daga rayuwarsa.

Sir Ahmadu Bello mutum ne mai sauƙin kai kuma mai son haɗin kan jama’a tare da son ganin ci gaban jama’a da ma ƙasa baki ɗaya. Maganganusa cike su ke da hikimomi. Dubi amsar da ya baiwa Dr. Azikiwe a lokacin da suka haɗu, Azikiwe ya ce da shi, “Ahmadu mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu mu haɗa kai…”, sai Sardauna ya bashi amsa da cewa: “A’a, mu dai fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninmu. Ni musulmi ne ɗan Arewa, kai kuma Kirista ne ɗan yammaci. Idan muka fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninmu za mu iya kawo haɗin kai a ƙasarmu”.

Sir Ahmadu Bello ya ce, “kusan tazarar mil 20 daga arewacin Sakkwato ɗaura da Kogi, akwai wani gari Raɓah. A nan aka haife ni a shekarar 1910”.

Salsalarsa:

Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ɗan ƙabilar Fulani ne, kuma shi jika ne a wajen Shehu Mujadaddadi. Sunan mahaifinsa Ibrahim Bello. Da kansa ya ce, “Mahaifina ɗan Abubakar ne, da aka fi sani da Atiku na Raɓah, wanda shi ne sarkin Musulmi na bakwai. Ya yi mulkinsa na tsawon shekaru huɗu (4) daga 1873. Mahaifinsa kuma shi ne Sultan Bello ɗan Shehu Usman Ɗanfodiye Mujadaddadi. Bello, wanda ya gaji jagoranci Musulunci a bayan rasuwar mahaifinsa kakan-kakana ne”.

Saboda haka kenan, Sir Ahmadu Bello ɗan Ibrahim ne, shi kuma Ibrahim ɗan Abubakar Atiku na Raɓah, shi kuma ɗan Sultan Bello shi kuma ɗan Mujadaddadi Shehu Usman. Don haka tsakaninsa da Shehu mujadaddadi rawani ko hula uku ce kacal. Wato mutane uku ne a tsakaninsa da Shehu mujadaddadi.

Ibrahim Bello wanda shi ne mahaifin Sir Ahmadu Bello ya kasance mutum ne jarumi wanda saboda jarumtakarsa wani shahararren mawaƙi na lokacinsa mai suna Zamnu ya yi masa kirari da Mai ƙafon karo a bayan da ya gwabza da Turawan mulkin mallaka iya ƙarfinsa. Sunan mahaifiyar Sir Ahmadu Bello Maimunatu wanda aka fi sani da Mamu.

Karatu:

An saka Sir Ahmadu Bello a makaranta tun yana ɗan shekara biyar, inda aka damƙa shi a hannun limamin Ravah Liman Abubakar wanda ya karantar da shi karatun Alƙur’ani da wasu littattafai.

Tun kafin zuwan Sir Ahmadu Bello hannun liman Abubakar ya iya karanta Fatiha da wasu gajerun Surori. Da zuwansa hannun liman sai aka ɗora inda aka tabbatar ya iya karanta gajerun surori tun da Fatiha zuwa Alamtarakaifa kamar yadda aka saba a makarantun Allo. Sir Ahmadu Bello ya sauke Alƙur’ani yana da shekaru goma sha biyu a duniya wato a tsawon shekaru bakwai kenan.

Bayan kammala saukar Alƙur’ani da ya yi, Sir Ahmadu Bello ya ɗora da karatun Littattafai inda ya samu nasarar kammala karatun littattafan Ahlari, Ishimawi da Risala a cikin shekaru biyu a wannan lokacin Sir Ahmadu yana da shekaru 14 kenan a duniya.

A shekarar 1924, Sir Ahmadu ya samu shiga makarantar boko a garin Sakkwato. Wato Sokoto Province School wacce ita ce ɗaya tilo makarantar boko a duk faɗin lardin. Bayan kammala karatunsa a Sakkwato ya samu nasarar shiga Makarantar Horas da Malamai ta Katsina. Wato Katsina Teachers Training College, Katsina.

Gagayyar Aiki:

Bayan kammala karatunsa a Katsina, Sir Ahmadu Bello ya zama malamin makaranta a Sakkwato Middle School wacce ita ce tsohuwar makarantarsa ta farko. Ya yi aiki a wannan makaranta daga shekarar 1931 zuwa 1934. Ayyukansa a wannan makaranta su ne karantar da English, Geometry da kuma Arabic inda daga baya ya zama mai kula da harkokin wasanni na makarantar.

Zamansa a wannan makaranta ya bashi cikakkiyar damar saka ido kan yadda ake gudanar da harkokin mulki a Sakkwato, ta hanyar halatar zaman da Sarkin Musulmi ke yi a fadarsa don gudanar da mulki, sannan kuma a lokaci guda shi ya zama kamar mai sadar da tsakanin masarauta da kuma Turawan mulkin mallaka kasancewarsa wanda ya ke jin yarensu.

A shekarar 1934 zuwa 1948, Sir Ahmadu Bello ya zamo hakimin Raɓah bayan naɗa shi da sarkin Musulmi na wancan lokacin ya yi, kamar yadda ya rubuta da hannunsa a cikin littafinsa, “Babban sauyi ya zo a 1934, lokacin da Sultan ya naɗa ni hakimin Raɓah dan na gaji ɗan uwana bayan rasuwarsa. Ina da shekaru 24 na zamo hakimi mafi ƙanƙanta da aka naɗa”.

Addininsa:

Sir Ahmadu Bello ya zamo mai matuƙar riƙo da addinisa da al’adarsa. A duk gurin da Ahmadu Bello ya ke kuma duk irin abin da ya ke yi, idan lokacin sallah ya yi yakan bar wannan aiki ya aiwatar da ibadarsa. Shi ne wanda ya samar da taken Arewacin Nijeriya na ‘Work and Worship’, ma’ana ‘A yi aiki a yi bauta’.

Sannan bai zamo mai bambantawa tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba. An ruwaito shi yana cewa, “a nan arewacin Nijeriya muna da mabambantan ƙabilu, yaruka da addinai waɗanda muka haɗu a tarihi guda, buƙata guda, da kuma shawara iri ɗaya. Abubuwan da suka haɗa mu sun fi waɗanda suka raba mu. Har kullum ina tunatar da mutanenmu cewa mu fa abu guda ne dan haka mu koyi haƙuri da addinan juna. Ba mu da niyyar fifita wani addini a sama da wani. Babban burinmu shi ne a kiyaye doka-da-oda, burinmu kuma shi ne kowa ya cikakken ’yancin gudanar da addininsa bisa karantarwar addinin nasa”.