Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Kula da Haƙƙoƙin Zamantakewa da Tattalin Arziki (SERAP) ta shigar da ƙarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu saboda gazawarsa wajen gudanar da bincike kan zargin cewa sama da Naira Tiriliyan 11 na nufin samar da ingantaccen wutar lantarki tun shekarar 1999 an sace su, ko kuma an karkatar da su zuwa aljihun gwamnati.
Biranen Nijeriya sun sha faɗawa cikin duhu yayin da aka ce na’urar wutar lantarki ta ruguje aƙalla sau uku a cikin watanni biyar, kuma sau 130 a cikin shekaru 7. A cewar Bankin Duniya, rashin ingantaccen wutar lantarki yana jawowa ‘yan kasuwa a Nijeriya asarar kusan dala biliyan 29 a duk shekara.
A ƙara mai lamba FHC/L/CS/1119/2022 da aka shigar a makon jiya a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman umarni da doka ta tilasta wa shugaba Buhari ya binciki yadda sama da Naira tiriliyan 11 na nufin samar da wutar lantarki na yau da kullum ɓace, wanda ake zargin gwamnatoci sun yi almubazzaranci tun 1999.
SERAP na kuma neman umarnin tilasta wa shugaba Buhari ya tabbatar da hukunta duk wanda ake zargi da hannu a cikin asusun wutar lantarki da ya ɓace, kamar yadda ya dace, tare da tabbatar da ganowa tare da ƙwato cikakken duk wasu kuɗaɗen jama’a da suka ɓata.”
SERAP ta yi nuni da cewa, “yana da amfani ga al’umma a tabbatar da adalci da kuma bin diddigin almundahana a fannin wutar lantarki, wanda ya jawo gazawar gwamnatoci wajen magance matsalar wutar lantarki da Nijeriya ke fama da ita a halin yanzu.”
