
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada biyayyarsa ta cigaba da bai wa mai gidansa, Shugaba Bola Tinubu goyon baya wajen sadaukarwa don hidimta wa al’ummar Nijeriya.
Shettima ya bayyana haka ne a Abuja yayin amsa saƙon taya shi murnar cika shekaru 59 a duniya, inda jaddada ƙarfin alaƙar da ke tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana jagorancin Tinubu ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata a matsayin hangen nesa don al’umma, wanda zai inganta rayukan ƴan ƙasa tun daga tushe.
Haka kuma ya yi godiya ga matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, gwamnoni, ƴan majalisa, ministoci, sarakuna da shugabannin addini bisa masa addu’o’i da fatan alheri.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce hakan salo ne na martaba salon jagorancin ƙasar, yana mai kira ga al’umma da su cigaba da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin junansu.
