Gwamnan Adamawa ya jagoranci kwamitin taron zartarwa na PDP

Spread the love

Jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da kwamitin mambobi 110 domin shirya babban taron zaɓen shugabannin jam’iyya da za a gudanar a ranakun 15 da 16 na watan Nuwamba, 2025 a Ibadan, Jihar Oyo.

An naɗa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa) a matsayin Shugaban Kwamitin, tare da Gwamna Ademola Adeleke (Osun) a Matsayin Mataimaki, da Gwamna Peter Mbah (Enugu) a matsayin Sakataren Kwamitin.

Haka kuma, Gwamna Bala Mohammed (Bauchi) ya Wakilci ƙungiyar Gwamnonin PDP, inda ya Jaddada haɗin-kai da jajircewar gwamnoni wajen ƙarfafa jam’iyyar.

Shugaban PDP na ƙasa, Amb. Iliya Damagum, ya bayyana taron a matsayin muhimmi wajen zaɓen sabbin jagororin jam’iyyar a kasa, inda ya buƙaci kwamitin da ya tabbatar da adalci da haɗin kai.

Da yake jawabi a madadin gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya yi alƙawarin zaburar da kwamitin wajen karfafa jam’iyyar da kuma shawo kan kalubale da ke gabanta.

By Babaji