
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Omala ta jihar Kogi, sun yi garkuwa da Hakimin Gundumar Bagaji Odo, David Wada.
An sace hakimin ne a lokacin da ya ke koma wa gida daga taron sarakuna a Abejukolo, wato hedikwatar ƙaramar hukumar a yankin Ojuwo Ugweche.
Wata majiya ta ce, lamarin ya auku ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin yayin da yake tafiya akan babur.
Sarkin masarautar Ƙaramar Hukumar, Onu na Ife, Boniface Musa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da ceto shi daga hannun ƴan bindigar.
Tuni kakakin ƴan sandan jihar, SP Williams Aya ya ce an baza jami’an tsaro tare da haɗin-gwiwar ƴan bindiga da mafarauta domin ceto hakimin.
