Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Maulidi

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 5 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun babbar sakatariya a ma’ikatar, Magdalene Ajani.

Miliyoyin al’ummar Musulmi ne ke bukukuwan Maulidi a Najeriya da kuma faɗin duniya a duk irin wannan lokaci, kowace shekara.

Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta buƙaci al’ummar ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji