Zamfara: APC ta soki Gwamna Lawal kan ɗaukar nauyin yunƙurin tsige Matawalle

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’ar APC ta Jihar Zamfara, APC ta zargi gwamnatin Gwamna Dauda Lawal bisa hanyar kafa ƙungiyoyi bisa abunda ta bayyana shawo kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori ƙaramin Ministan Tsaro, Dr Bello Mohammed Matawalle daga muƙaminsa.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Yusuf Idris Gusau ya yi wannan ikirarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau yau Lahadi.

Jami’iyyar ta zargi Gwamna Dauda da abin da ta bayyana ta hanyar amfani da masu zanga-zanga, shugabannin addinai da ma’aikata daga wurare daban-daban musamman a faɗin Arewacin Najeriya da wasu sassan kudu don tayar da hankalin ‘yan Najeriya kan a tsige karamin ministan tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle.

“Waɗannan ƙungiyoyin da aka tattara suna amfani da makami mafi gamsarwa, musamman rashin tsaro don yaɗa bayanan ƙarya don shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige ƙaramin ministan Tsaro Bello Mohammed Matawalle.”

“A cikin wani ikirari, ɗaya daga cikin irin waɗannan ‘yan kwangila ya tabbatar kwanan nan cewa ya karɓi rabin biliyan na kuɗi daga gwamnan saboda yaɗa bayanan ƙarya akan Matawalle”.

A cewar jam’iyyar, gwamnatin jihar Zamfara ta saki rikakken ɗan ta’adda mai suna Musa Kamarawa daga gidan yari, wanda aka kama bisa umarnin Matawalle lokacin da yake gwamna don yaɗa farfagandar a cire ministan.

Jam’iyyar ta kuma zargi Gwamna Dauda da ɗaukar nauyin wasu mutane daga kudu maso gabas, zuwa majalisar dokoki ta ƙasa don neman a cire Matawalle a shekarar bara.

A cewar jam’iyyar, wasu mata daga cikinsu waɗanda aka bai wa Naira miliyan 20 suma sun je Hedikwatar DSS da ke Abuja don wannan dalili, duk da haka basu cimma buƙatar su ba.

“Mun lura cewa tsoro gwamna Dauda Lawal yake yi don ganin akwai yiwuwar dawowar Matawalle a matsayin gwamna a 2027, sakamakon ficewar manyan jiga-jigan Jam’iyyar ta PDP zuwa APC a jihar”. Jam’iyyar ta ce.

Jam’iyyar ta yi kira ga hukumomin tsaro, majalisar shari’a ta ƙasa, ƙungiyar lauyoyi NBA da ƙungiyoyin fararen hula su zo su tabbatar da binciken yadda aka saki Musa Kamarawa daga gidan yari don ya kare gwamna Dauda Kuma gashi shari’ar sa bata ƙare ba.

By ukarofi