Bello Turji ya tabbatar da yin tattaunawar sulhu da gwamnatin Matawalle

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, ya tabbatar da cewa an yi zaman sulhu tsakaninsa da gwamnatin Zamfara ta lokacin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro.

Saidai ya musanta batun karɓar Naira Miliyan 30 da kuma baburan hawa daga gare ta.

Turji ya faɗi haka ne cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Asabar.

Gabannin wannan dai, Musa Kamarawa wanda gwamnatocin Sakkwato da Zamfara suka wakilta don sasantawa da ƴan bindiga a Arewa maso yammacin Nijeriya, shi ne ya bayyana cewa gwamnatin Matawalle ta bai wa Turji Naira Miliyan 30.

A cewar Turji, “Ban taba mallakar ko da miliyan biyar ba, abinda nake yi ba don kai na nake yi ba, kuma ba’a taɓa bani miliyan 30 ba.”

Ya kuma zargi Kamarawa da cin amanar tattaunawar da suka yi da shi, abin da ya kira da “ƙarya da faɗan abinda ba haka shi ne haƙiƙanin gaskiyar al’amari ba”.

Kazalika, ya zargi ƴan siyasa a jihohin Zamfara da Sakkwato da bada gagarumar gudumawa ga halin rashin tsaro da ke addabar shiyyar tun gabannin Matawalle ya kama mulki, yana mai zargin ƴan banga da takura wa al’ummar Fulani.

A ƙarshe, Turji ya nesanta kansa daga kowace irin jam’iyyar siyasa ko kuma wani ɗan siyasa da wata manufa ta ayyukansa.

By Babaji