
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar Lahadi ne wani jirgin gida mai tashin angulu na kamfanonin Flybird Airlines ya karci ƙasa a Filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, lamarin da ya girgiza al’umma.
Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa fasinjoji 11 ne ke cikin jirgin a lokacin da abin ya faru ciki har da jami’an jirgin su uku, waɗanda suka taso daga Abuja.
An samu tsaikon ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe yayin da jirgin ke ƙoƙarin sauka.
Sannan, an samu sauƙin al’amarin ne a lokacin da aka ciro mutanen da ke cikin jirgin ba tare da an samu jikkata ko rauni daga gare su ba.
Hukumar filin jirgin tuni ta tabbatar da tsaurara tsaro wajen baza jami’an agajin gaggawa da kuma yin bincike akan musabbabin faruwar al’amarin.
