Komawar Gwamna Kefas APC ta kawo ƙarshen mulkin PDP na shekara 26 a Taraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajista a APC ya kuma karɓi katin zama ɗan jam’iyya, alamar shirin sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam’iyar mai mulki.

Shugaban APC na mazabarsa a Ƙaramar Hukumar Wukari, wanda kuma ya miƙa masa katin, shi ne ya yi wa gwamnan rajistar a ofishinsa da ke Jalingo a jiya Lahadi.

Da yake jawabi bayan karɓar katin, Gwamna Kefas ya ce matakin ya yi daidai da shirin da ya kammala na sauya sheƙa zuwa APC bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyar.

Ya ce, an jinkirta sauya shekar ne tun da farko saboda sace ɗalibai a jihohin Kebbi da Neja.

Gwamnan ya ƙara da cewa, za a sanar da sabuwar ranar sauya shekar a nan gaba.

Komawar gwamnan APC ta nuna cewa an sami gagarumin sauyi a Taraba inda kowane gwamna da aka taɓa yi a jihar a baya, ɗan PDP ne tun daga dawowar dimukraɗiyya a 1999.

Haka kuma, wannan ya nuna cewa APC tana da jimillar gwamnoni 27 a faɗin Nijeriya.

By Babaji