Gwamnan Katsina ya taya DC Saulawa murnar samun muƙamin Provost Marshal

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya mataimakin kwanturola na hukumar kwastam ta ƙasa (Nigeria Customs Service), DC Sanusi Tasiu Saulawa, murnar naɗa shi a matsayin Acting Provost Marshal na hukumar.

Gwamnan ya bayyana naɗin a matsayin wata babbar shaida ta ƙwarewa, riƙon amana, da nagartar aiki da DC Saulawa ya nuna a tsawon lokacin da yake hidima ga ƙasa.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a Muhammad Kaula ya sanya wa hannu ya ce Gwamnan ya bayyana cewa wannan karin girma na nuna yadda ake ƙara yarda da ‘yan asalin Jihar Katsina a manyan muƙamai na ƙasa, musamman a ɓangarorin tsaro da tattalin arziki.

“Muna alfahari da ganin ɗaya daga cikin ‘ya’yanmu ya samu wannan muhimmin matsayi a ƙasa. DC Sanusi Saulawa ya nuna ƙwarewa, ɗa’a da jajircewa a aikinsa. Muna da yaƙinin zai sauke wannan nauyi cikin girmamawa da ƙwarewa,” in ji Gwamnan.

Ya ƙara da cewa yana da cikakken yaƙini cewa DC Saulawa zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta ɗa’a da bin ƙa’idoji a cikin hukumar kwastam ta ƙasa.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa Jihar Katsina na ci gaba da samar da ƙwararrun ma’aikata masu kishin ƙasa, wadanda ke wakiltar jihar da Najeriya gaba ɗaya da mutunci a hidimar gwamnati.

“Wannan nasara ta nuna irin jajircewa da daidaito a aikinka. Ka ci gaba da ɗaga tutar Katsina da Najeriya sama,” ya ƙara da cewa.

Haka zalika, Gwamna Raɗɗa ya yabawa babban kwanturola na hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, bisa yadda ya nuna amincewa da DC Saulawa, yana mai cewa hakan alama ce ta ingantaccen shugabanci da ke bai wa nagartattun ma’aikata dama.

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya ba DC Saulawa hikima, lafiya da nasara a sabon muƙaminsa.

By ukarofi