
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ADC, ta ayyana tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya ci zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa yayin babban zaɓen 2027.
Atiku ya samu jimillar ƙuri’u 1,846,370, wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, wanda ya samu ƙuri’a 504,117.
Haka ma ɗan kasuwa Mohammed Hayatu-Deen, wanda ya zo na uku da ƙuri’a 177,120.
Wannan sakamako ya nuna cewa Atiku shuni ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, a wani yanayi da masu sharhi ke bayyanawa a matsayin gagarumar ci-gaba a ɓangaren adawa.
Da yake jawabinsa na karɓa jim-kaɗan bayan bayyana sakamakon, Atiku ya yaba wa jam’iyar bisa ƙoƙarinta wajen kiyaye dokokin dimukraɗiyya da harkokinta a matakin cikin jam’iyya.
Ya kuma koka da ƙalubalen da jam’iyyun adawa da jagororin siyasa ke fuskanta a sassan ƙasar, yana mai cewa wajibi ne a ba martabobin dimukraɗiyya kariya da ƙarfafa su.
