
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya yi kira ga babban abokin karawarsa a zaɓen fidda gwani da aka yi jla jihar kwanan nan, wato tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Mohammed Adam Abubakar da ya cigaba da zama a jam’iyyar domin taimaka wa kai ta ga nasara a zaɓen 2027.
Tsohon sufeton ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar SDP bayan ya yi rashin nasara a zaɓen fidda gwani a karawarsu da Wadada.
Mohammed Abubakar ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su tafi tare da shi domin tabbatar da nasarar burinsa na tsaya wa takarar gwamna a jihar.
Da yake jawabi yayin ziyarar godiya ga Gwamna Abdullahi Sule a Lafiya, Sanata Wadad ya ce tsohon IGPn zai fi dacewa da cigaba da kasancewa ɗan APC a madadin shiga wata jam’iyya.
Ya kuma bayar da misali da lokacin da ya rasa tikitin takarar a shekarar 2018, inda ya cigaba da zama a jam’iyyar kuma ya jagoranci majalisar kamfen ɗin da ta kai Gwamna Sule ga nasara.
