2027: Shettima ya kirayi jagororin siyasa su kauce wa kalaman tunzuri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya yi kira ga jagororin siyasa da ‘yan ƙasa da su tunkari zaɓen 2027 cikin hikima da ƙaurace wa dukkan abin da zai janyo fitina, yana mai gargaɗin tunzura ka iya haddasa tashin-tashina a Nijeriya.

Shettima ya kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi na aiki tuƙuru wajen magance matsalolin tattali ta gyare-gyare da wasu shirye-shirye da ke gudana.

Ya bayyana haka ne a jiya Laraba bayan kammala sallar Idi a filin Ramat Square da ke Maiduguri, Babban birnin Jihar Borno.

A wata sanarwa da Kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana cigaba da ƙoƙarin ganin ta shawo kan matsalolin tattali da suka jefa al’umma cikin matsi da ƙarfafa tsaro da faɗaɗa damarmaki ga ‘yan Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma kirayi al’ummar Nijeriya da su cigaba da haƙuri da ba wa gwamnatin goyon baya akan ƙoƙarinta na dawo da daidaiton al’amura a ƙasar.

Haka kuma, Shettima ya roƙi da a riƙa yin addu’o’in samun zaman lafiya da ɗorewa a sassan ƙasar, yana mai cewa haɗin kai babban ginshiƙi ne ga ci-gaban ƙasa.

By Babaji