Mateta ya taimaka wa Crystal Palace lashe kofin Turai a karon farko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace da ke ƙasar Ingila ta lashe kofinta na farko na Nahiyar Turai a birnin Leipzig bayan doke Rayo Vallecano ta Sifaniya da ci 1 da 0 a wasan ƙarshe na gasar UEFA Conference League.

Palace ta zama ƙungiya ta farko da ta lashe irin kofin a yunƙurin farko cikin shekaru 38.

Ɗan wasa Philip Mateta ne ya samu damar zura ƙwallon ne a minti na 51a lokacin da mai tsaron gidan Vallecano, Augusto Batalla ya buge ƙwallon da Adam Wharton ya farmake shi da ita.

Wannan nasara ta nuna muhimmancin ɗan wasan ga ƙungiyar, wanda a ya yi yunƙurin tafiya AC Milan a watan Junairu da hakan ya ci tura.

By Babaji