Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babu hanyar da bata Shiguwa a dukkanin faɗin Jihar Katsina a yanzu dalilin samuwar tsaro a cewar mataimakin gwamnan jihar Katsina Farouk Lawal.
Ya bayana haka ne a lokacin da Sarkin Katsina ya kai masa gaisuwar babbar sallah a tsohuwar fadar gidan gwamnatin Katsina.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ya bayyana irin sauƙin matsalar tsaro da aka samu a jihar Katsina inda ya ce “babu hanyar da bata shiguwa saboda samuwar sauƙin matsalar tsaro”
Ya ƙara da cewa daga farkon gwamnatinsu zuwa yanzu, an samar da malamai sama da dubu bakawai don ganin an ƙara haɓɓaka harkar ilimi a dukkannin sassa na faɗin jihar Katsina.
Ya kuma bayyana irin shirye shiryen da gwamnati take samarwa ga manoma na faɗin jihar Katsina domin su samu sauƙi tare da haɓɓaka tattalin arziki na jihar baki ɗaya.
A jawabin sa Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman yayi kira ga al’umma da su haɗa kai tare da kauce ma hassada domin cigabar jihar Katsina baki ɗaya.
Irin wannan gaisuwar ban girma ga alada Sarkin na kaiwa a kowace shekara a ƙaramabda babbar sallah da ranar hawan Sarki.
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya canza sunan hawan daga hawan Bariki zuwa hawan Sarki.
