‘Yan bindiga sun kashe darakta da kansila a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

‘Yan bindiga sun kashe Jamilu Sani Jangebe, daraktan tsare-tsare na ƙaramar hukumar Talata Mafara, da Kansila mai wakiltar Marabar Jangebe, Hon Muslim Jangebe bayan shafe kwanaki a hannun su.

Shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara, Hon. Yahaya Yari, ya tabbatar da kisan a lokacin da yake yi wa iyalan mamatan ta’aziyya.

Ya ce majalisar ta yi ƙoƙari sosai don ganin an saki jami’an biyu amma ba ta yi nasara ba.

A cewar Hon. Yari, masu garkuwa da mutanen sun bayyana ƙarara cewa ba su da niyyar sakin kowa daga garin Jangebe.

“Sun gaya mana cewa duk wanda ya faɗa hannunsu, matuƙar dai ya fito daga garin Jangebe, ba sa son kuɗin fansa. Za su kashe shi kawai,” in ji shugaban.

Ya ƙara da cewa majalisar karamar hukumar ta bi duk wata hanyar da ake da ita don yin shawarwari kan sakin waɗanda abin ya shafa, amma ‘yan bindigar suka nuna rashin amincewa su.

Hon. Yari ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamatan, sannan ya roƙi Allah maɗaukakin sarki da ya bai wa iyalansu ƙarfin jure rashin da aka yi.

Ya kuma sake nanata ƙudirin majalisar na yin aiki tare da hukumomin tsaro don kare mazauna yankin da kuma tabbatar da an kamo waɗanda suka aikata kisan don gurfanar dasu a gaban kuliya.

Jamilu Sani Jangebe yana aiki a matsayin daraktan tsare-tsare a ƙaramar hukumar ta Talata Mafara, yayin da kansilan da aka kashe yana wakiltar mazaɓar Jangebe a majalisar dokokin ƙaramar hukumar.

Wannan lamari shi ne na baya bayan nan a cikin jerin hare-hare da sace sacen da ake dangantawa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke aiki a sassan jihar Zamfara, inda al’ummomin karkara da jami’an gwamnati ke ƙara zama waɗanda ‘yan ta’adda ke kai wa hari.

By ukarofi