Ashiru Kudan ya zama ɗan takarar gwamnan Kaduna a ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar ADC ta zaɓi Isa Ashiru Kudan a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Hon. Ashiru tsohon ɗan takarar gwamna ne a Kaduna har sau biyu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP.

Ashiru Kudan, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Maƙarfi/Kudan ne, ya yi nasara ne bayan samun ƙuri’a 86,113.

Sai tsohon Kwamishinan Ilimi a gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i, wato Jafaru Sani, wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 29,580.

Sauran ‘yan takarar sun haɗa da tsohon Kwamishinan Ilimi a gwamnatin yanzu ƙarƙashin Uba Sani, Professor Muhammad San-Bello, wanda ya sami 13,559; Ahmed Tijjani, ƙuri’a 13,550; da kuma Shuaibu Mikati mai ƙuri’a 10,819.

A shekarar 2019 ne El-Rufa’i ya kayar da shi a zaɓen gwamnan jihar. Haka ma a zaɓen 2023, inda Uba Sani ya kada shi bayan samun ƙuri’a 719,000.

A jawabinsa bayan sanar da sakamakon, Hon. Ashiru Kudan ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna masa, yana mai alƙawarin haɗa kan dukkan mambobin jam’iyyar wajen samar da shugabanci nagari ga al’umma.

By Babaji