Hajjin 2026: NAHCON ta tabbatar da kiyaye dokokin tsaron abinci da ƙaddamar da binciken jigilar mahajjata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta jaddada ƙoƙarinta na tabbatar da kiyaye walwala a harkokin aikin hajji, inda ta sanar da tsauraran matakai akan tsaron abinci da ƙaddamar da bincike akan masu aikin jigila da aka zarge su da wulaƙanta mahajjata.

A wata sanarwa da NAHCON ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce abincin dare da dama a ranar 27 ga watan Mayu, 2027, an ƙi karɓar su saboda rashin cika sharuɗɗan kula da killacewa.

An ruwaito cewa, an ƙi amincewa a karɓe su ne da haɗin-gwiwar hukumomin lafiya na Saudiyya bisa nazari akansu.

Ta ƙara da cewa, a sakamakon haka ne aka samar wa mahajjatan da al’amarin ya shafa ƙwarya-ƙwaryar kumallo.

Hukumar ta bayyana cewa ‘yan kwamiti sun ba wa manajoji ba’asin al’amarin yayin da Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya umarci kwamitin tsaro da ya gudanar da bincike akan masu aikin abincin da kuma ‘yan kwangilar da ke da alaƙa da su.

Kazalika, hukumar ta ce an fara shirye-shiryen tabbatar da gaggauta mayar wa mahajjatan da hakan ya shafa kuɗaɗen abincin da aka ƙi amsar.

A wani ɓangare kuwa, Ambasada Yusuf ya umarci kwamitin cibiyar tsaro da ya bincike masu aikin jigila da aka zarga da kawo wasu mahajjata da ba su da rajista da kuma wulaƙanta wasu mutane, yana mai cewa za a hukunta dukkan wanda aka samu da da hannu a laifukan da ake zargin nasu a kai.

By Babaji