Abin da ya sa nake son a koro ‘yan wasan Real Madrid daga gasar Kofin Duniya – Mourinho

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sabon kocin ƙungiyar Real Madrid, Jose Mourinho ya yi fatan a koro ‘yan wasan ƙungiyar daga gasar Kofin Duniya na 2026 da wuri saboda su mayar da hankali akan wasannin gabanin sabuwar kaka cikin tsanake.

Mourinho ya bayyana haka ne a wata hira ta wani shiri da aka gudanar ta BeastModeOn inda ya tattauna akan muhimman ƙalubalen da manyan ƙungiyoyi suke fuskanta yayin da ake buga manyan gasa na ƙasa da ƙasa.

Daga cikin ‘yan wasan ƙungiyar da ke buga gasar Kofin Duniya na 2026 akwai Kylian Mbappe, Vinicius Junior, Aurelien Tchouameni, Antonio Rudiger da kuma Marc Cucurella.

Yayin da yake ake sa ran manyan ‘yan wasansa ka iya zuwa babban mataki a gasar, Mourinho na fatan fara shirye-shiryen sabon kakar wasa ba tare da mafi muhimmancin ‘yan wasa ba ga ƙungiyar.

A cewarsa, ya fi fifita wasannin gabanin gasa akan wasu wasanni don haka yake fatan a sallami ƙasashen da ‘yan wasan nasa suke buga wa da wuri domin so koma wa ƙungiyar.

‘Yan wasa Mbappe da Tchouameni na da muhimmanci ga tawagar Faransa, kamar yadda Vinicius yake ga Brazil. Haka ma, Rudiger ga ƙasar Jamus da Cucurella ga Sifaniya, waɗanda shigarsu cikin tawagogin ka iya haifar musu da jinkirin koma wa Madrid.

By Babaji

Leave a Reply