Allah-wadai da kisan Ummulkhairi

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk fa shi ne illar kamfen ɗin nan na ‘yan ikira irin gayawa jini na wuce kan Umummlkhairi a Marabar Jos duk miyagu sun yi gum kan kisan don haka su ke so Arewa ta zama.

Duk ƙoƙarin nunawa mutane muhimmancin bincike da bin doka da oda, ya zama abin zagi da sharri daga Zallawa don burinsu birane da ƙauyuka su zama dandalin ɗaukar doka a hannu tamkar dai yadda ya auku ga Malamar Islamiyya Umumulkhairi a Marabar Jos a Kaduna inda daga tambaya ba wata shaida kawai mutane su ka zartar da hukuncin kisa har da ƙona gawa kuma har nemawa kansu uzuri su ke yi wai kowa ya san a na sace mu su yara. Ba su kama mai sacewa mu su yara ba amma sun kashe uwar yara sun jefa kananan ’ya’yanta cikin garari da juyayi.

Ba bazalle ko daya da ya nuna damuwa kan wannan aika-aika ko don ba mamaki Ummulkhairi malamar Islamiyya ce. Haka mutanen nan ke kawar da kai ga masu tare hanya su kashe matafiya don bambancin addini ga uwa uba kotu ta yankewa wani dan ina-da-jini Zidane Kajuru hukunci amma Zallawa su ka yi wuf su ka ce dan gwagwarmayar ƙwatar ‘yanci ne a kyale shi. Kajuru fa ya ja zuga ya yi sanadiyyar shekar da jinin fiye da mutum 60+ a irin wannan yanayi na ɗaukar doka a hannu.

Mun tuna yadda Askarawan Zamfara su ka kama babban shehin malaminmu shugaban Izala na Gusau Sheikh Abubakar Hassan Mada haka kurum don ƙiyayya su ka je gefen gari su ka yi masa yankan rago bayan ƙarairaya ma sa gabobi. Shin akwai ma mai misali da shi? Ai kamar an shafe tarihinsa tun da ba damuwar ‘yan kwangilar rusa Arewa ba ne.

Wasu ma ‘yan gayawa jini na wuce a Sokoto ai sun yi tsalle kamar dangin shaidan su ka yi mummunan kisan g!illa ga Malam Usman Buda kawai don wata muhawara da gangancinsu ya sa su ka jahilta kuma da wannan al’adar ta ɗaukar doka a hannu.

Ina kira ga duk ‘yan Arewa masu kishin zaman lafiya su kara ƙaimi wajen yaƙi da muguwr aguguwar fitina da Zallawa ke neman tayarwa don biyan muradunsu na Midibelawa da ‘yan awaren nan da ke yi msu su zuga-zugi fiye da na uwar maƙera!

A guji ɗaukar doka a hannu don hakan ya sa zaluntar marar sa laifi bila-adadin.

Duk wanda ya kalli wa in ma hoto ko faifan bidiyon yaran da a ka kama don tuhumar yin kisan gilla ga Malama Ummulkhairi a Maraban Jos sun yi siffar ‘yan figaggun yaran da ‘yan bazata ke yaudara don tada fitinar ƙabilanci. Na taɓa ba ku labarin wasu matasa da na gamu da su a wani shago a Abuja da ‘yan bazata su ka juyawa kwakwalwa. Duk irin fasalin su ɗaya da waɗannan yara da tamkar jira su ke yi a buɗe ƙofar kyasta ashana su ce ga fetur. Kuma alamu na nuna irin su ne da ba su san doka ba kan yi wuf su yayata faifan bidiyon ‘yan ta’adda.

Haƙiƙa don amfanin ajin irin waɗannan matasa da kan zama ‘yan arufta mu kan yi rubutun nan na ankararwa ga mummunar manufar ‘yan bazata ga Arewa da ke son yankin ya hargitse don cikawa ‘yan aware burinsu tun na zamanin Ojukwu da kuma Midibelawa.

Maƙiya Hausawa da musulunci na bullo da logogi kusan kullum don ruruta fitinar ƙabilanci don ingiza musulmi su shiga ɗauki ba daɗi kan juna don mafarkin korar addinin daga Arewa da shunfuda gadon Yammawan mullkin mallaka. Haba me jiya ta yi balle yau a ɗauri kashi ko a ɓata igiya. Tabbas mutanen nan ‘yan ta’addan yanar gizo ba za su taɓa cin nasara ba. Idan kuma su na da ja ga fili ga doki.

Babban abin da kan tura irin wannan fitina ba kamar yaɗa labarun ƙarya na haddasa ƙiyayya tsakanin al’umma da gangan da maƙiya yankin Arewa ku kullawa ba dare da rana.

Cikin makircin da masu zummar tada fitina a Arewa ke yi shi ne na dawo da batun kisan gilla ga marigayi Sarkin Gobir Alhaji Muhammad Isa Bawa ta hanyar ingiza jama’a da cusa makircin ƙabilanci a akasin.

Gabanin fara wannan kwangilar ta ƙaryar Hausa Zalla, akwai cikakkiyar alama masu kamfen ɗin ba su san cikakken sunan masarautar Gobir ba balle ma a je ga batun marigayi Alhaji Muhammadu Isa Bawa wato Sarkin Gobir na Gatawa. Ko yanzu mutanen nan ba su san ina ne Gatawa da mukaman sarauta na masarautar Gobir ba. Kai ko gaggan ‘yan kwangilar ba su iya furta sunan marigayin daidai ba don gwarawa ne na yayatawa a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo. Mutanen da wasu ma wallahi ba su taba ziyartar Arewa maso yamma ba amma don makirci za ka ga an lakkana mu su, su rubuta “a na ta kashe mu sai mun jira an karar da mu ne?..”

Kimanin wata biyu da su ka wuce ‘yan kwangilar ta tada yakin ƙabilanci a Arewa sun yi wa hoton marigayi da miyagun iri su ka ɗauka a daji FILTER da wasu zayyane-zayyane na AI su ka bukaci duk ‘yan gayyar arufta su yi ta yayata hotunan don kar bakin cikin gillar ya dan yi sassauci a zuciyar jama’ar ƙasa. Haƙiƙa mutanen nan ba su da izini ko hurumin yin hakan daga ƙasar Gobir ko fadar mai alfarma Sarkin musulmi. Lallai ne a takawa waɗannan ‘yan barandar IPOB birki daga amfani da hotunan marigayi mai martaba.

Hatta naɗa sabon Sarkin Gobir Alhaji Abdullahi Dan Galadima bai yi wa ‘yan kwangilar dadi ba don sun so a bar masarautar haka don cigaba da amfani da yanayin wajen zafafa makircin da su ke kullawa. Ba ko mutum ɗaya da ya taya Alhaji Abdullahi Dan Galadima murna.

Tun a shekara ta 2024 sojoji su ka cafke wanda a ke zargin da gillar Bako Wurgi Bayan raunuka da ya samu ya shiga asibiti a Shinkafi don samun magani. Kazalika babban mai gidan ‘yan ta’addan Halliru Sububu ya daɗe da shekawa lahira. Duk mai bin rubutun da na ke yi ya san lokacin da mu ka yi watsi da jita-jitar wai dan majalisar dokokin jihar Sokoto Aminu Boza Gobir ne ya ba da Naira miliyan 5 don sace marigayin. Tun da zargin ya fito ne daga miyagun ya zama da tababa don tantiran makaryata ne.

Duk mai son zaman lafiya mai kuma nazari zai yi wancakali da ‘yan ƙaryar Hausa zalla da ke yayata hoton marigayi da ba su da wata alaka da shi hasalima don bambancin addini ba zai zama su na ƙaunarsa ba don Musulmi ne. Kai sun ma yi murna da akasin don sun samu makamin farafaganda a soshiyal midiya.

Duk mai yayata hotuna ko bidiyon da ‘yan ta’adda su ka ɗauka to wa in ma abokin burminsu ne ko ya na taya su kawo fitina a ƙasa.

Masu tsarawa Zallawa wato ‘yan farafagandar ruruta fitinar ƙabilanci manufofi su dinka rigar Hausawa don saukin yaudarar Musulmi a Arewa su shiga kiyayyar ƙabilanci, ba su yi nazari mai kyau kan tasirin Musulunci da ke zama tsakanin mutum ne da Allah ba tsakanin mutum da sarakuna, malamai ko zuwa kan Shehu Mujaddadi ba.

Tun zamanin da wasu marubuta marar sa tauhidi su ka juya koyarwar Shehu zuwa wai Jihadi ne na wata ƙabila, makiya Musulunci ke marmarin ganin Musulmi sun dau lamarin a haka kuma in sun yi ridda ma ba laifi ba ne.

Shi ya sa wannan sabuwar kwangila ta dinka rigar Hausawa ba ta yi nasara a tsakanin masu tauhidi ba sai fasiƙai da sauran ‘yan bazata inda ba ma amfanin shawartarsu su jingine Musulunci don dama ba layinsu ba ne sun fi ma iyayen gidan na su kin jinin addinin.

Masu tsara manufofin nan THINK TANK na Zallawa na ƙoƙarin keɓe Yausawa daga Musulunci don a wajensu ai Fulani masu jihadi su ne musulunci don haka Hausawan da su ke son zugawa da wai an danne mu su ‘yanci, su shiga ɗauki ba dadi kan doron ƙabilanci amma da Musulmi Fulani. Su kuma ‘yan Zallawa sun san ba zai yiwu su iya kiran Hausawa su bar Musulunci da wai a ka yaudare su da shi ba don haka su ka shiga yaɗa faragandar izgilanci wai akwai addinin Fodiyanci kuma Shehu Mujaddadi shi ne Annabi na addinin. Wannan logar ma ta kasa sayuwa don duk Musulmi sun san yarfe ne kawai na fasiƙai. Ko a ‘yan kwanakin nan sun ɓullo da kamfen ɗin ta faifan bidiyo wai a na zuwa bautar Shehu a Sokoto! Shin da wa da wa ke zuwa wannan ziyara da su ke murdawa da sunan bauta? Kai mutanen nan sun raina Musulmi amma ba za su ci nasara ba har abada kan wannan bahagon mafarkin nasu.

KAMMALAWA

A nan ya na da muhimmanci hukumomin gwamnati su riƙa gudanar da bincike don daƙile makircin masu son haddasa fitinar ingiza jama’a su ɗau doka a hannu. Kowa zai iya faɗawa tarkon masu ɗaukar doka a hannu don yadda ake ta yayata kiyayya a tsakanin al’ummar da ta share shekaru aru-aru ta na zaune tare a waje ɗaya kuma zumunci ya ƙullu ta dukkan ɓangarorin rayuwar yau da kullum. Sarakunan gargajiya, malaman addini da marubuta duk na da gudunmawa wajen takawa guguwar nan birki.

By ukarofi