
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan wasa Folarin Balogun ya koma cikin tawagar ‘yan wasan Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya tsoma baki akan al’amarinsa na wasan da ya gabata.
Saidai Balogun ya gaza taimaka wa ƙasar kai wa zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe a karon farko tun a 2002 a gasar Kofin Duniyar da ke gudana a Nahiyar Amurka bayan da Belgium ta lallasa ta da ci 4 da 1.
Tawagar Amurka ta fara gasar ne cike da ƙwarin-gwiwar kasancewarta a gida inda ta samu tikitin hayewa zagaye na gaba kai-tsaye daga na rukunin-rukuni.
A wasan zagayen ‘yan 32 ne Folarin Balogun ya samun jan kati, wanda daga bisani aka soke sakamakon shiga tsakani da Trump ya yi gabanin wasan ƙasar da Belgium.
