Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta yi Allah wadai da kama Dakta Bishir Kurfi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Daraktan ƙungiyar kare hakin ɗan Adam a Najeriya (Amnesty International) Malam Isah Sunusi ya yi Allah wadai da kama Dakta Bishir Kurfi da Gwamnatin Katsina da jami’an ‘yan sanda suka yi.

Malam Isah Sunusi wanda ya faɗi haka a wata hira da yayi a wata kafar sadarwa ya ce tsare Dakta Kurfi da akayi ya saɓa doka,take haƙƙin biladama da nuna amfani da ƙarfin iko wajen aikata ba daidai ba.

Ya ce ƙungiyar ta gano kama Dakta Kurfi ya aza ayar tambaya akan wasu abubbuwa da ya zargi gwamnatin Katsina da aikatawa, bai kamata ace an kama shi ba.

“Kamata yayi gwamnati tayi bincike akan zargin domin a tabbatar ko a musanta bisa hujja ko bincike na gaskiya,”Inji Sunusi.

Ba wai kawai ayi amfani da ‘yan sanda da kotu a kama shi ba a cewar Isah Sunusi.

Ya bayyana fargabar irin wannan mataki da aka ɗauka a kansa na karya doka da take haƙƙin ɗan Adam ƙarshen ta a na so ayi amfani da shi domin hana wasu da suke sha”awar fitowa su aza ayar tambaya akan yadda ake kula da kare rayukan mutane daga ‘yan fashin daji suce suma abinda zai faru da su kenan.

Isah Sunusi ya ce tun shekarar 2020 ƙungiyar su ke bibiyar abubuwan da suke faruwa akan musgunawa masu fafutuka,masu kare haƙƙin ɗan Adam da ‘yan jarida idan sunyi magana akan gazawar gwamnati wajen kare rayukan jama’a.

Sai ya yi kira ga gwamnati kada ta wahalar da Dakta Bishir Kurfi ta sake shi ,su mai da hankali akan yaƙi da ‘yan fashin daji da sauran ‘yan ta’adda da suka hana alummar Jihar Katsina sakat.

A maimakon su wahalar da rufe masa baki, ƙungiyar ta ce kamata ya yi su mai da hankali da ƙarfin su wajen warware matsalar tsaro wanda nauyin ne ke kan su ba takurawa mutane da cin zarafin masu yin suka ba.

By ukarofi

Leave a Reply