Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a jam’iyyar PDP, Hon. Tijjani Rabi’u Alhassan Mai Zare, ya bayyana cewa idan Allah ya ba shi damar wakiltar al’ummar Gwale, zai bai wa ilimi, matasa, mata, ƙananan yara da kuma harkar ruwan sha muhimmanci a ƙaramar hukumar.
A zantawarsa da Blueprint Manhaja, Mai Zare ya ce takararsa ta Allah ce, kuma duk wani al’amari sun bar shi ga Ubangiji. Ya ƙara da cewa suna roƙon Allah ya zaɓa musu abin da ya fi alheri.
Hon. Tijjani Mai Zare ya bayyana cewa ya samu ilimi da tarbiyyar da suka taimaka masa wajen fahimtar rayuwa da kuma kyakkyawar mu’amala da al’umma.
Ya kuma ce, “Ina son maraya ya daina jin kamar ya rasa mahaifansa, domin duk lokacin da na ji cewa ni ma maraya ne, sai na tuna cewa mahaifana biyu Allah ya yi musu rasuwa.”
Ya ƙara da cewa kasancewar iyayensu da kakanninsu sun kasance ƴan kasuwa tare da taka rawa a siyasa, hakan ya koya masa darussa masu yawa game da gaskiya, riƙon amana da kuma hidimar jama’a.
Hon. Tijjani Mai Zare ya ce shi ɗan kasuwa ne, kuma kasuwanci ya gaje shi ne daga kakanninsa. Ya bayyana cewa tun bai kai shekara 20 ba iyayensa suka buɗe masa shago domin ya fara sana’a, a don haka ya ce ƴan kasuwa su ma za su yi dariya.
A cewarsa, waɗannan tarbiyya da gogewar da ya samu tun yana ƙarami ne suka ƙara masa ƙwarin gwiwar neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano domin wakiltar al’ummar ƙaramar hukumar Gwale tare da tabbatar da an gudanar da wakilci nagari.
