Matafiya sun shiga mawuyacin hali yayin da manyan motoci da aikin titi suka haifar da cinkoso a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar ranar Asabar ne matafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna suka haɗu da tsaiko a sakamakon wani cinkoson ababen hawa a yankin Kateri, lamarin da ya jefa su cikin halin rashin tabbas game da makomar zirga-zirgarsu.

Wakilin Blueprint.ng da ke wajen ya ruwaito cewa, cinkoson ya shafi masu zirga-zirga na ɓangarorin titin guda biyu, inda aka ga wani dogon layi na jerin gwanon motoci a yankunan babbar hanyar.

Ya bayyana cewa, halin ya fi zama matsi ga masu zuwa Jere da Abuja inda haɗakar aikin gina titi da yawaitar manyan motoci suka haifar da cinkoson.

An ga yadda jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) da sojoji suke ƙoƙarin shawo kan matsalar ta hanyar kula da zirga-zirgar da kuma ƙoƙarin samar da dama ga ababen hawan da al’amarin ya shafa dom su cigaba da sufurinsu.

Hanyar Kateri zuwa Jere zuwa Zuba na da muhimmanci musamman don ganin yadda take a matsayin wani ɓangare na aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

By Babaji

Leave a Reply