Fasinjoji da manyan motoci sun shiga matsi bayan ruwan sama ya shafe wata gada a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fasinjoji da dama da motoci ciki har da tireloli sun shiga halin takura a hanyar Limankara zuwa Gwoza da ke Ƙaramar Hukumar Gwozan Jihar Borno bayan wani mamakon ruwan sama ya karya wata gada da ke kan titin.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu daga cikin fasinjojin sun shafe tsawon kwana biyu a hanyar cikin halin matsi yayin tafiya daga Mubi a Jihar Adamawa, waɗanda suka ce halin ya jefa ɗaruruwan mutane cikin yunwa da rashin samun damar zuwa inda za su samu sauƙin al’amarin.

Wasu daga ciki – Daniel Adamu da Abubakar Audu sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa mamakon ruwan sama da aka zabga ya sanya al’umma na fuskantar tsanani yayin tafiya kan hanyar, waɗanda suka ce tana fuskantar ƙalubalen rashin tsaro. An ga yadda fasinjoji da motoci suke ƙoƙarin tsallake wata ambaliya bayan ruwan sama ya shafe gadar hanyar Limankara zuwa Gwoza a Borno.

A cewar fasinjojin, an bayar da kwangilar gina gadar amma ba a kammala ba, lamarin da ya taimaka wajen jefa masu zirga-zirga a yankin cikin takura sakamakon mamakon ruwan saman wanda aka shafe kwana biyu ana yi.

Akan haka ne fasinjojin suka yi magiya ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno da su gaggauta kai ɗauki domin suna fuskantar mawuyacin hali yayin zirga-zirga a titin. Sakamakon lalacewar gadar, fasinjoji da ke tafiye-tafiye daga Yola zuwa jihar Borno yanzu sun koma bin hanyar Damaturu zuwa Gombe, wadda ta kai tsawon kilomita 500.

By Babaji

Leave a Reply