Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC), Farfesa Attahiru Jega, da mai kula da cocin Katolika na jihar Sakkwato, Rabaran Matthew Kukah, sun yi kira da a ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓe, tabbatar da riƙon amana a harkokin siyasa da kuma samar da ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin ’yan siyasa da al’umma, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sun bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa na jama’a da Cibiyar Kukah (TKC) da kuma Cibiyar Nazarin Majalisa da Dimokuraɗiyya ta ƙasa (NILDS) suka shirya a Abuja.
Tarayyar Turai ce ta bayar da tallafin kuɗi tare da sauran masu ɗaukar nauyi wajen gudanar da taron, a ƙarƙashin shirinta na tallafa wa ingantaccen shugabanci na dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Tallafin na daga cikin manyan tsare-tsaren da Tarayyar Turai ke aiwatarwa ta hanyar Shirin Tallafa wa Dimokuraɗiyya da Shugabanci Nagari a Nijeriya (EU-SDGN), wanda aka ƙaddamar domin bunƙasa shugabanci bisa tsarin dimokuraɗiyya, tabbatar da riƙon amana a hukumomi da kuma ƙarfafa shigar ’yan ƙasa cikin harkokin mulki.
Taken taron shi ne, “Sadarwar Siyasa, Tsaron Zaɓe da Makomar Dimokuraɗiyyar Nijeriya”. Taron ya samu halartar jami’an zaɓe, masana ilimi, ƙwararru a fannin sadarwar siyasa da kuma shugabannin ƙungiyoyin farar hula.
An shirya taron ne domin nazarin yadda saƙonnin siyasa, gaskiya da riƙon amana a hukumomi, da kuma tsaron zaɓe ke tasiri wajen gina amincewar jama’a da tsarin zaɓe gabanin zaɓen 2027.
Da yake jawabi a wajen taron, Rabaran Kukah ya ce makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya za ta dogara matuƙa da matakai da matakan da ake ɗauka a halin yanzu. Ya bayyana cewa dimokuraɗiyyar Nijeriya tana da makoma, amma irin makomar da za ta samu ya danganta ne da abin da ’yan ƙasar za su yi a wannan lokaci.
Malamin addinin ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su riƙa tantance ’yan takara da manufofin da suka gabatar yayin yaƙin neman zaɓe. Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa neman cikakken bayani daga gare su kan muhimman matsalolin ƙasa kafin su ba su damar riƙe muƙaman gwamnati.
A nasa jawabin, Farfesa Jega ya jaddada muhimmancin ingantacciyar hanyar sadarwa da hukumomin gudanar da zaɓe ke amfani da ita wajen gina amincewar jama’a da tsarin zaɓe. Jega, wanda ya jagoranci zaman tattaunawar, ya ce yadda hukumar zaɓe ke isar da saƙonni ga jama’a na iya yin tasiri kamar yadda matakan da take ɗauka suke da tasiri.
Tsohon shugaban na INEC ya ce wajibi ne hukumomin zaɓe su riƙa fitar da bayanai cikin lokaci, a bayyane kuma bisa sahihanci, domin yadda suke sadarwa na taka muhimmiyar rawa wajen tsara ra’ayin jama’a game da matakan da suka ɗauka da kuma sakamakon zaɓe. Ya ce wannan batu ya fi zama wajibi a halin yanzu, musamman ganin yadda yaɗa bayanan ƙarya da saƙonnin siyasa masu karo da juna ke iya karkatar da fahimtar jama’a game da harkokin zaɓe.
Jega ya kuma yi kira da a ɗauki nauyin kare sahihancin zaɓe a matsayin alhakin kowa da kowa. Ya ce ’yan siyasa, ƙungiyoyin farar hula, ’yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki duk suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kare tsarin dimokuraɗiyya.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Farfesa Jibrin Ibrahim, Farfesa Okechukwu Ibeanu, Kwamishinan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, Malam Kudu Haruna, mai rajin kare haƙƙin jama’a, Aisha Yesufu, da kuma Samson Itodo na ƙungiyar Yiaga Africa.
Masu jawabi a taron sun tattauna musamman kan yadda sadarwar siyasa ke tasiri ga gudanar da zaɓe, nauyin da ya rataya a wuyan ’yan siyasa wajen tsara tattaunawar da ake yi a tsakanin al’umma, da kuma muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin tinkarar barazanar da ke fuskantar tsaro da sahihancin zaɓe.
Taron ya zama wata muhimmiyar dama ga jami’an zaɓe, masana ilimi da ƙungiyoyin farar hula wajen nazari da sukar ƙalubalen da dimokuraɗiyyar Nijeriya ke fuskanta a yayin da ake tunkarar zaɓen 2027. Mahalarta taron sun jaddada cewa gudanar da sahihin zaɓe ba ya dogara ga ƙwarewar fasaha da ingantattun matakan tsaro kaɗai. Sun ce amincewar jama’a, gaskiya da riƙon amana a hukumomi, sadarwar siyasa mai nagarta da kuma jajircewar ’yan ƙasa wajen neman a yi wa zaɓaɓɓun shugabanni hisabi, duk suna da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar dimokuraɗiyyar Nijeriya.
