Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata gobara ta tashi a sashen sayar da magungunan gargajiya na Babbar Kasuwar Potiskum da ke Jihar Yobe, inda ta ƙone rumfunan kasuwanci 56, shaguna shida da kuma wani masallaci. Gobarar ta kuma jawo asarar kayayyaki da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin nairori.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ce ta bayyana hakan a cikin wani rahoto da ta fitar bayan gudanar da bincike domin tantance girman barnar da gobarar ta yi a ƙaramar hukumar Potiskum. Hukumar ta ce, tawagarta ta kai ziyara wurin da gobarar ta tashi domin duba irin asarar da aka yi, tare da jajantawa ’yan kasuwar da abin ya shafa da sauran al’ummar kasuwar.
SEMA ta nuna damuwa kan yadda gobara ke ci gaba da faruwa a wannan sashe na kasuwar, tana mai cewa irin wannan iftila’i ya taɓa faruwa a wurin kimanin shekaru biyar da suka gabata. Hukumar ta ce bayan aukuwar gobarar da ta gabata, ta shiga tsakani ta hanyar gyara rumfunan da suka lalace, domin bai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa damar komawa gudanar da harkokinsu. Da take bayyana sabuwar gobarar a matsayin abin damuwa matuƙa, hukumar ta jaddada buƙatar samar da matakai masu ɗorewa domin hana sake aukuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.
Daga cikin matakan da SEMA ta ba da shawarar ɗauka akwai girka na’urorin kashe gobara a kasuwar da kuma tabbatar da kula da su akai-akai, samar da wuraren samun ruwa cikin sauƙi, gudanar da binciken tsaro a kai a kai, da kuma wayar da kan ’yan kasuwa a kai a kai kan hanyoyin kariya daga gobara da kuma yadda za su tunkari aukuwar ibtila’in gaggawa. Hukumar ta kuma yi kira ga shugabannin kasuwar, ƙungiyoyin ’yan kasuwa, Majalisar ƙaramar Hukumar Potiskum da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen inganta kayayyakin kariya daga gobara da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro a kasuwar.
SEMA ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da inganta shirye-shiryen tunkarar iftila’i, kai agajin gaggawa da kuma rage haɗarin aukuwar bala’o’i a faɗin jihar.
