Gwamnatin Tinubu ta ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa shirye-shiryen samar da kuɗaɗen gudanar da noma, da nufin ƙarfafa samar da isasshen abinci, ƙara yawan amfanin gonar da ake nomawa a cikin gida da kuma inganta ayyukan ƙananan manoma a faɗin Nijeriya.

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya fitar ranar Lahadi. Sanarwar ta ce, shirin tallafin da ake aiwatarwa ta hannun Bankin Noma na Nijeriya (BOA) ya riga ya taimaka wa ƙananan manoma sama da 500,000 a jihohi 16, ciki har da mata sama da 70,000.

Ta ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya kuma amince da shirin ƙara jarin Bankin Noma na Nijeriya da Naira tiriliyan 1.5, domin faɗaɗa damar manoma na samun kuɗaɗen gudanar da noma da kuma tallafa wa noman hekta 500,000 a ƙarƙashin shirin Ajandar Sabunta Fata. Kwamitin ya bayyana cewa tallafin gwamnatin bai tsaya ga bayar da lamuni ga manoma kawai ba, domin ya haɗa da samar musu da ingantattun iri, takin zamani, injinan noma, hanyoyin ban ruwa, wuraren ajiya da kuma damar kai amfanin gonarsu kasuwanni.

A cewar sanarwar, Asusun Tallafa wa ƙananan Manoma da Sarƙar Darajar Amfanin Gona na Ajandar Sabunta Fata, wanda aka ware wa Naira biliyan 250, na samar da kuɗaɗen tallafi ta hannun kamfanonin tattara manoma wuri guda.

Waɗannan kamfanoni ne ke da alhakin yin rajistar manoma, raba musu kayan aikin gona, ba su shawarwari da horo kan dabarun noma, da kuma haɗa su da kasuwannin da za su sayar da amfanin gonarsu. Sanarwar ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin, an raba kusan buhunan takin zamani miliyan 2.5 da kuma buhunan ingantattun iri 300,000 ga manoma.

Ta ce shirin na da burin tallafa wa manoma miliyan biyu tare da samar da buhunan takin zamani sama da miliyan 10.

Jihohin da suka ci gajiyar wannan shiri sun haɗa da Kaduna, Kano, Katsina, Neja, Borno, Gombe, Taraba, Adamawa, Yobe da Bauchi. Haka kuma, Bankin Noma na Nijeriya na aiwatar da shirin tabbatar da mafi ƙarancin farashin amfanin gona, wanda aka ware wa Naira biliyan 200, domin kare manoma daga illar sauyin farashin kasuwa da kuma tilasta musu sayar da amfanin gonarsu cikin gaggawa a farashi mai rahusa. A ƙarƙashin wannan shiri, bankin ya sayi kusan tan 170,000 na masara, shinkafa, dawa da rogo, domin ƙarfafa kasuwannin sayar da amfanin gona.

Dangane da shirye-shiryen da aka tsara domin tallafa wa wasu nau’o’in noma na musamman, kwamitin ya yi tsokaci kan Shirin Tallafa wa Masu Noman Albasa, wanda aka samar tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Manoma, Masu Sarrafa da ’Yan Kasuwar Albasa ta Nijeriya (NOPPMAN). ƙungiyar tana wakiltar manoman albasa sama da 11,800.

An tsara shirin ne domin samar wa manoma ingantattun iri da takin zamani, taimaka wa masu sarrafa albasa da kuɗaɗen sayen amfanin gonar, tare da gina wuraren ajiya da na’urar sanyaya kaya masu amfani da hasken rana, domin rage asarar albasa bayan girbi.

A tsarin samar da kuɗaɗen gudanar da shirin, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma za su biya kashi 30 cikin 100 na kuɗin kayan aikin noma, yayin da Bankin Noma zai ɗauki nauyin sauran kashi 70 cikin 100. Dangane da shirin ƙara jarin bankin da Naira tiriliyan 1.5 kuwa, kwamitin ya ce matakin zai ƙarfafa ƙarfin bankin wajen samar da lamuni mai sauƙin samu ga manoma, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma, masu sarrafa amfanin gona, masu tattara amfanin gona da sauran ’yan kasuwa da ke cikin sarƙar ayyukan noma.

Ya ƙara da cewa, ƙarin jarin zai bai wa bankin damar tallafa wa manyan ayyukan zuba jari a fannin noma, faɗaɗa ayyukansa zuwa yankunan manoma da ba sa samun isasshen tallafi, tare da samar da warin kuɗaɗen da za su taimaka wajen bunƙasa noman cikin gida.

Sanarwar ta kuma lissafa wasu shirye-shiryen tallafi da suka shafi manoma, mata da matasa. Daga cikinsu akwai samar da kuɗaɗen noman rani, injinan noma, farfaɗo da noman citta, tallafa wa ƙungiyoyin haɗin gwiwar mata da kuma bunwasa kiwon kaji na kasuwanci.

A ƙarƙashin shirin noman rani, Bankin Noma na aiki tare da ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN) domin samar da tsarin tallafi da zai kai ga manoma 400,000 a zangon noman shekarar 2026.

Shirin ya wunshi noman alkama a fili mai girman hekta 120,000, da kuma wasu hekta 300,000 da za a noma shinkafa, masara, dawa, gero, rogo da waken soya.

Haka kuma, Shirin Farfaɗo da Noman Citta na Nijeriya ya taimaka wa manoma 3,200 a yankin Kachia da ke Jihar Kaduna, ta hanyar samar musu da irin citta da ba ta da cutar da ke lalata amfanin gonar. Shirin ya kuma samu nasarar farfaɗo da buhunan citta sama da 9,000 domin amfani da su wajen samar da iri. Ana kuma shirin faɗaɗa aikin zuwa filayen noma masu girman hekta 20,000 a jihohi 16.

Bankin ya kuma sa aniyar tallafa wa mata aƙalla 50,000 a faɗin ƙasar, ta hanyar samar da lamunin noma ga ƙungiyoyin haɗin gwiwarsu, tare da inshorar amfanin gonar da kuɗin ruwa na kashi tara cikin 100. Ana aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ma’aikatun Harkokin Mata da na Noma na Tarayya. A fannin samar da injinan noma kuwa, kwamitin ya ce an rarraba taraktoci 1,571 zuwa jihohi 23 a ƙarƙashin Shirin Ƙasa na Bunƙasa Amfani da Injinan Noma na Ajandar Sabunta Fata.

Ana sa ran taraktocin za su taimaka wajen amfani da injina wajen noma filayen da yawansu ya kai hekta miliyan 1.2. Manoma kuma za su samu damar amfani da injinan ta hannun ƙwararrun masu samar da ayyukan noma da injina. Haka kuma, kwamitin ya bayyana cewa gwamnatin ta ƙaddamar da wani shirin samar da wutar lantarki domin bunƙasa ayyukan tattalin arziki, wanda aka ware wa Naira biliyan 385.

Shirin zai samar da babura masu ƙafafu uku masu ɗaukar kaya guda 44,000 masu amfani da wutar lantarki, da kuma famfunan ban ruwa guda 100,000 masu amfani da hasken rana. Ana sa ran shirin zai amfani iyalan manoma 500,000. A cewar kwamitin, waɗannan shirye-shiryen tallafi na nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na mayar da noma wani babban ginshiƙi na bunƙasar tattalin arzikin ƙasa, samar da isasshen abinci da kuma samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply