A bana ne Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa ƙaimi ga yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, shekarar bana shekara ce da Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa kaimi ga yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS.

Bisa goyon bayan ɓangarori daban daban, ƙasar Sin ta gudanar da taruka da bukukuwa fiye da 70 cikin nasara a matsayin ƙasar dake shugabancin BRICS a wannan karo, matakin da ya taimaka wajen yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS a fannoni daban daban.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, an samu sakamako mai kyau a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da mu’amalar al’adu, da samun bunƙasuwa mai dorewa, da kiwon lafiyar al’umma da sauransu, waɗanda suka ba da gudummawa ga raya haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen BRICS, da aza tubalin shirya taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 14.

Fassarawa: Zainab