Sin za ta taimakawa Tanzania bunƙasa ilimin sana’o’in hannu

Daga CMG HAUSA

Ƙasashen Sin da Tanzania, sun ƙaddamar da wani shirin hadin gwiwa dake da nufin bunƙasa ilimin sana’o’in hannu, ta hanyar samar da sabon mizani a ɓangaren, a ƙasar ta gabashin Afrika.

Shirin kawance kan ilimin sana’o’in hannu tsakanin Sin da Afrika ne ya ɗauki nauyin sabon shirin na nazari da inganta mizanin ƙwarewar aiki da aka ƙaddamar a ranar Laraba, inda zai gudana ƙarƙashin kulawar majalisar kula da ilimin fasahohi da sana’o’in hannu ta ƙasar Tanzania (NACVET).

A cewar Jiang Yilin, sakatare janar na shirin kawancen Sin da Afrika, jimilar kwalejojin koyar da sana’o’in hannu 43 na ƙasar Sin ne za su shiga kashin farko na shirin da ya ƙunshi mizanin sana’o’in hannu daban daban guda 54.

A nasa ɓangaren, babban sakataren NACVET Adolf Rutayuga, cewa ya yi, shirin zai sauƙaƙa raya ilimi da horon sanan’o’in hannu a Tanzania, haka kuma zai shimfida tubalin kafa sabon mizanin ilimi.

Ya ƙara da cewa, shirin zai kuma taimaka wajen samar da ɗimbin ma’aikata masu basira, da tabbatar da waɗanda za a yaye a bangaren, sun cimma buƙatun kasuwar duniya da ɗaukaka matsayin masana’antun ƙasar.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa