Ya kamata a sanya binciken kare haƙƙin ɗan Adam a Amurka cikin ajanda

Daga CMG HAUSA

Yayin gudanar da taron ƙolin kwamitin kare haƙƙin dan Adam na MƊD karo na 50 wanda aka gudanar kwanakin kaɗan da suka gabata a Geneva, ƙasar Cuba ta fidda sanarwa a madadin ƙasashe kusan 70, inda ta nuna adawa da yin shisshigi a harkokin cikin gidan ƙasar Sin ta hanyar fakewa da batun haƙƙin dan adam. Bugu da ƙari, sama da karin ƙasashe 20 ne suka yi jawaban nuna goyon baya ga ƙasar Sin.

Kusan ƙasashe 100 ne suka yi jawabai game da ƙasar Sin ta hanyoyi daban-daban, inda hakan ke nuna cewa, al’ummar ƙasa da ƙasa, musamman kasashe masu tasowa, sun fahimci makirci da yin baki biyu da Amurka da wasu ƙasashen yammacin duniya ke yi kan batutuwan dake shafar haƙƙin dan adam, kuma sun bayyana cikakkiyar matsayarsu na yin adawa da Amurka da ƙasashen yamma, inda suke amfani da batun haƙƙin ɗan Adam a matsayin makaman siyasa wajen kai hari kan abokan adawarsu.

A haƙiƙanin gaskiya, kowa ya sani cewa idan ana magana kan batun take haƙƙin dan Adam, ƙasar Amurka ta kasance a matsayin kanwa uwar gami. Yayin da ƙasar Amurka ke ƙalubalantar sauran ƙasashe kan batun haƙƙin dan adam, ya kamata ƙasashen duniya su kalli batun a mahanga mafi girma. Batun binciken kwamitin kare haƙƙin ɗan Adam na MƊD kan yanayin take haƙƙin ɗan Adam a Amurka, ya kamata a sanya shi cikin ajanda ba tare da bata lokaci ba.

Fassarawa: Ahmad