Majalisar Kogi ta dakatar da wasu mambobinta

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta tsige tare da dakatar da wasu ‘ya’yanta kana ta maye gurbinsu da takwarorinsu nan take.

‘Yan majalisar da lamarin ya shafa sun haɗa da: Rt. Hon. Ahmed Muhammed (Mataimakin Kakaki), Hon. Bello Hassan Balogun (Shugaban Masu Rinjaye), Hon. Idris Ndako (Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye) da kuma Hon. Edoko Moses Ododo (Babban Mai Tsawatarwa).

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Yahaya Bello na jihar ya sha kaye a zaɓen fitar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa da Jam’iyyar APC ta gudanar.

Majiyarmu ta ce ɗaukar wannan mataki da majalisar jihar ta yi na da nasaba da ƙin zaɓen Gwamna Yahaya Bello da wasu daliget ɗin jihar suka yi yayin zaɓen fidda gwanin.

Manhaja ta kalato cewa, Majalisar ta naɗa Hon. Alfa Momoh Rabiu, ɗan majalisa mai wakiltar yankin Ankpa II, a matsayin sabon Mataimakin Kakakin Majalisar.

Sauran mambobin majalisar da suka maye guraben takwarorin nasu da aka dakatar su ne, Hon. Muktar Bajeh, Okehi (Shugaban Masu Rinjaye), Umar Isah Tanimu, Lokoja 1 (Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye), Enema Paul, Dekina/Okura (Mataimakin Mai Tsawatarwa), sai kuma Ahmed Dahiru, Okene II a tsayin Babban Mai Tsawatarwa.

‘Yan majalisar su 17 ne suka sanya hannu kan batun tsige Hon. Ahmed Mohammed da kuma dakatar da sauran mambobi ukun da lamarin ya shafa.

Wasu majiyoyi na zargin cewa, hakan ya faru ne a sakamakon nuna ƙarfin ikon da ake yi tsakanin Mataimakin Gwmanan Jihar, David Onoja da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Muhammed Asuku, inda wasu ‘yan jihar ke zargin kowannensu na ƙoƙarin shirya kansa ne don yin mulki a 2024.