Abdu Maikaba ya zama sabon kocin Kno Pillars

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta naɗa Abdullahi Maikaba a matsayin sabon kocinta.

Maikaba ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da kungiyar da ake kira “Sai Masu gida” daga kakar 2023/2024 zuwa 2024/2025.

Kocin zai yi aiki tare da Abubakar Abubakar da ake kira Senior da Ahmad Garba Yaro Yaro da Gambo Muhammad da kuma Auwalu Abbas a matsayin mai horar da masu tsaron gida.

Da yake ƙaddamar da kocin a ofishinsa, mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo, ya buƙace shi da ya zage damtse domin farfado da martabar ƙungiyar.

Mataimakin gwamnan, ya taya shi murna tare da bayyana naɗin nasa a matsayin wanda ya dace ganin irin ɗumbin kwarewarsa a harkar koyar da ƙwallon ƙafa a ƙungiyoyin daban-daban a Nijeriya.

Mataimakin Gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da bai wa ƙungiyar goyon baya domin ganin an cimma burin da aka sanya a gaba, sannan kuma ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin Kano za ta kara ƙaimi wajen gyaran filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar mata Kano.

Ya yaba wa shugabannin ƙungiyar da ’yan wasan ƙungiyar bisa kwazon da suka nuna wanda ya sa ƙungiyar ta koma gasar Firimiya.

Da yake mayar da martani, Abdullahi Maikaba ya gode wa mahukuntan ƙungiyar da suka amince da shi sannan ya yi alƙawarin tabbatar da amincewar da aka yi masa.

A bara ne Pillars ta faɗi daga gasar Firimiya ta ƙasar, wadda ta koma buga gasa mai daraja ta biyu, wadda za ta buga babbar gasar tamaula ta bana a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *