Abinci shi ne tushen rayuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM YAYA

MƊD da hukumomin ƙasa da ƙasa su kan fito da jerin tsare-tsare da manufofi, baya ga wasu ranaku da ake keɓewa a duk shekara, don nazartar irin nasarori da ma akasin haka da ɓangaren aikin samar da abinci a duniya ke fuskanta. Sai dai annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta haifar da illoli da sauran matsaloli ga ɓangaren samar da abinci a duniya, inda alkaluma ke nuna cewa, kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa.

Sai dai yayin da wasu ƙasashe ke nuna halin ko’in kula kan wannan lamari, ita kuwa ƙasar Sin a matsayinta na babbar ƙasa mai tasowa, wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ganin duniya ta amfana da duk wata irin ƙwarewa da fasahohinta, musamman ƙasashe masu tasowa, baya ga taimakawa ƙasashe masu tasowa, wajen inganta ayyukansu na noma ta hanyoyi daban daban. 

Ƙasashen Afirka da dama, kamar Najeriya sun amfana da irin fasahohin noma da ma irin shinkafa mai inganci daga ƙasar Sin, matakan da suka taimaka matuƙa wajen kara yawan shinkafar da ake nomawa a irin waɗannan ƙasashe fiye da shekarun baya.

Bayanai na nuna cewa, daga lokacin da aka ƙaddamar da haɗin gwiwar ƙasashe masu tasowa ƙarƙashin hukumar samar da abinci da gona ta MƊD wato FAO, a shekarar 1996, ya zuwa yanzu, ƙasar Sin ta tura masana ayyukan gona da injiniyoyi kusan 1100 zuwa ƙasashe sama da guda 40 na nahiyar Afrika, da Asiya, da kudancin Pacific, da yankin Caribbean da sauran sassan duniya.

Abin da ya ƙara nuna muhimmancin da ƙasar Sin ke bayarwa ga batun samar da abinci, kasancewarsa tushen rayuwa, sabanin yadda wasu ƙasashe ke buya abinci, inda suke amfani da shi a matsayin makami na haifar da yunwa a duniya.

Ƙarƙashin kulawar hukumar FAO, kwararrun ƙasar Sin sun yi aiki tukuru wajen daga matsayin fasahohin ayyukan noma sama da 1000 a ƙasashe masu yawa a fannoni daban daban na aikin gona, da kiwon dabbobi da halittun ruwa, da noman rani, da kuma sarrafa kayan amfanin gona, lamarin da ya taimaka wajen bunƙasa ƙaruwar samar da irin shuka a gonaki daga kaso mai tarin yawa. Haka kuma kusan manoma 100,000 a ƙasashen duniya ne suka samu irin wannan horo daga masanan na ƙasar Sin.

A gabar da duniya ke fama da tasirin annobar COVID-19, baya ga matsaloli na sauyin yanayi da shi ma ke yiwa ɓangaren aikin gona illa ta wasu fannoni. Sai dai kamar kullum, bikin magaji ba ya hana na magajiya, ma’ana hakan ba zai hana masu ruwa sa tsaki ɗaukar matakan da suka dace na ganin an wadata duniya da abinci ba.

Bayanai na nuna cewa, akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai ko matakan ƙashin kai da wasu ƙasashen yamma suka ɗauka. Matakai da tsare-tsare da ƙasar Sin ke bijiro da su ƙarƙashin haɗin gwiwar Sin da kasashen Afirka, sun taimaka matuka wajen ƙara samar da abinci da ma dabarun noma kala-kala a sassan nahiyar. Masana na cewa, ƙasashen Afrika za su iya amfani da hulɗar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da ƙarancin sinadarai masu gina jiki, da kuma haɓaka tattalin arzikin mazauna karkara.

A cewar shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin, dalilin da ya sa JKS mai mulkin ƙasar ke samun cikakken goyon baya daga al’ummar ƙasar shi ne, tana tsayawa kan ƙoƙarin tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, musamman manoma. Wannan na nuna cewa, idan har ana son wadatar da ƙasa da abinci, ya kamata mahukunta su taimakawa manoma don su samu karin kuɗin shiga, da raya ƙauyuka, da kuma ci gaba da zamanintar da aikin gona. Don haka, abinci shi ne tushen rayuwa, amma ba makami na siyasa ba.

By Editor