Daga CMG HAUSA
Kwanan baya, jawabin wata tsohuwar jakadar ƙasar Amurka a ƙasar Sin da kafofin yada labaru suka gabatar, ya sake sanya mutane sun ƙara sanin halayyar wasu Amurkawa. An ruwaito cewa, Sheila Carey, ƙaramar jakadar Amurka mai kula da tattalin arziki da siyasa a birnin Guangzhou da Andrew Chira, sun yi karin bayani kan maƙarƙashiyar Amurka kan batun Xinjiang a wata liyafa a asirce a shekarar 2021, a yunƙurin neman samun goyon bayan kamfanonin Amurka, inda suka ce, “Lallai ba matsala a jihar Xinjiang. Mun san haka, amma muna ƙara gishiri kan batun wai tilastawa a yi aiki a Xinjiang, da kisan kiyashi a jihar, tare da sukar ƙasar Sin kan batun hakkin dan Adam. Nufinmu shi ne jefa gwamnatin Sin cikin mawuyacin hali baki ɗaya.”
Matakan da Amurka take dauka kan batun Xinjiang sun wuce zaton mutane, alal misali, ƙirƙiro ƙarya, da kara gishiri da kuma shafa wa ƙasar Sin baƙin fenti. Turawa kan ce, idan ka yi karya sau ɗaya, to, za ka ci gaba da yin ƙarya sau dari 1. Amma ƙarya ba ta musunya haƙiƙanin halin da ake ciki a Xinjiang ba, inda ake samun kwanciyar hankali da wadata, sa’an nan mazauna wurin suna jin daɗin zamansu.
Alƙaluman da mahukuntan jihar Xinjiang suka gabatar sun nuna cewa, a watan Janairu zuwa Mayu na bana, an samar da sabbin guraben aikin yi dubu 263 a Xinjiang, wanda ya kai kashi 57.17 cikin kashi 100 bisa jimillar sabbin guraben aikin yi a bana. Yayin da ake fuskantar barazana wajen raya tattalin arziki da kuma yaƙi da annobar COVID-19 a ƙasar, Xinjiang ta yi ƙoƙari sosai domin cimma wannan manufa. Al’ummomin Xinjiang masu yawa sun yi nuni da cewa, suna aiki tukuru domin samun zaman rayuwa mai kyau, ba wanda ya tilasta musu.
Wasu suna shakkar cewa, me ya sa Amurka ta mai da hankali kan musulman da ke zama a Xinjiang kawai, duk da cewa, musulmai fararen hula masu yawa da ba a iya ƙidaya yawansu ba sun rasa rayukansu cikin yaƙe-yaƙen da Amurka ta gudanar da sunan “yaki da ta’addanci”? Wajibi ne ‘yan siyasan Amurka su yi karin bayani kan ƙaryarsu kan Xinjiang.
Fassarawa: Tasallah Yuan
